Rahoto: Yadda Aka Kashe Mutane 2,360 a Borno, Filato da Wasu Jihohin Najeriya

Rahoto: Yadda Aka Kashe Mutane 2,360 a Borno, Filato da Wasu Jihohin Najeriya

  • Kamfanin Beacon Security ya tabbatar da kisan mutum 2,360 da kuma sace wasu 1,175 tsakanin Janairu zuwa Maris na shekarar 2026
  • A yankin Arewa maso Gabas ne ya aka fi kashe mutane, inda aka rasa rayuka 801, yayin da Arewa maso Yamma ta fi yawan wadanda aka sace
  • Borno ce kan gaba a kashe-kashe da mutum 546, yayin da jihar Kaduna ta fi fuskantar garkuwa da mutane, inda aka sace kimanin mutane 296

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Wani sabon rahoto daga kamfanin Beacon Security, wanda ke nazarin matsalolin tsaro a yankin Sahel, ya nuna cewa an samu gagarumar taɓarɓarewar tsaro a Najeriya a cikin watanni uku na farkon shekarar 2026.

Rahoton ya bayyana cewa duk da matakan da jami'an tsaro ke ɗauka, hare-haren ƴan bindiga da ƙungiyoyin ta'addanci na ci gaba da ƙaruwa.

Kara karanta wannan

Amurka da Iran na tsagaita wuta, matatar Dangote ta sauya farashin fetur a Najeriya

Rahoto ya nuna cewa an kashe fiye da mutane 2,360 a sassan Najeriya daga Janairu zuwa Maris, 2026.
Wata mata zaune a kusa da kangon gidanta a kauyen Kawuri, jihar Borno bayan harin Boko Haram da ya yi ajalin mutum 70. Hoto: STRINGER / Getty Images
Source: Getty Images

Yadda aka kashe mutane 2,360 a Najeriya

Binciken ya nuna cewa an kashe jimillar mutum 2,360 a sassan ƙasar daban-daban cikin wannan ƙanƙanin lokaci, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Waɗannan hare-hare dai sun haɗa da ayyukan ƴan fashin daji, masu garkuwa da mutane, da kuma ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP waɗanda suka daɗe suna addabar sassan ƙasar.

Rahoton ya fayyace cewa yankin Arewa maso Gabas ne ya fi fuskantar asarar rayuka, inda aka kashe mutum 801. Wannan na da alaƙa da ƙaruwar hare-haren ƙungiyoyin jihadi, musamman harin da aka kai garin Ngoshe a watan Maris yau.

Ga adadin mutanen da aka kashe a sauran yankunan:

  • Arewa ta Tsakiya - 762
  • Arewa maso Yamma - 508
  • Kudu maso Gabas - 157
  • Kudu maso Kudu - 64
  • Kudu maso Yamma - 58

Haka kuma, jihar Borno ce ke kan gaba, inda aka kashe mata mutane 546, sai jihar Filato mai mutum 203, da kuma jihar Kwara inda aka kashe mutum 198.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da muka sani kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran

Hakazalika,a jihar Benue an kashe mutane 174, sannan aka kashe wasu 125 a jihar Katsina, yayin da jihar Kebbi ta rasa mutane 122.

Matsalar garkuwa da mutane a Najeriya

Baya ga kashe-kashe, rahoton matsalar tsaron, wanda Beacon Security ya wallafa a shafinsa na LinkedIn, ya nuna cewa garkuwa da mutane ta zama babbar hanyar samun kuɗin fansa ga ƴan bindiga.

Daga ranar 1 ga Janairu zuwa 31 ga Maris, 2026, an sace mutum 1,175 a faɗin Najeriya. Yankin Arewa maso Yamma ne ya fi kowanne yanki yawan mutanen da aka sace, inda aka dauke mutum 661.

'Yan bindiga na ci gaba da cin karensu ba babbaka duk da kokarin jami'an tsaron Najeriya.
Sojojin Najeriya a kan tankar yaki yayin da suka nausa cikin daji. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

A bangaren jihohi, ga jerin jihohin da aka fi sace mutanensu:

Wannan rahoto ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke ƙoƙarin shawo kan matsalolin tsaro ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomin tsaron.

Sai dai alkaluman da kamfanin ya fitar sun nuna cewa akwai sauran rina a kaba wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ƴan Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Ya haura N1,215: Ƴan kasuwa sun sanar da sabon farashin man fetur a Najeriya

'Yan bindiga sun hallaka janar din soja

A wani labari, mun ruwaito cewa, ana fargabar wani babban jami’in soja, Birgediya-Janar a Najeriya ya rasa ransa bayan harin Boko Haram a jihar Borno.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne yayin da mayaƙa suka kai farmaki da yawa cikin dare.

Rahotanni sun ce sojoji sun kashe mayaƙa da dama a yayin artabun, yayin da jama’a suka bayyana alhini kan rasuwar jami’an tsaro da aka rasa a harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com