Najeriya na dab da Rugujewa? Minista Ya Faɗi Gaskiyar Halin da Ƙasa Ke ciki
- Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya musanta rahotannin da ke cewa Najeriya na dab da rugujewa, yana mai cewa ƙasar na samun ci gaba
- Gwamnati ta bayyana cewa jami'an tsaro sun samu nasarori a yaki da ta'addanci, yayin da a gefe daya, tattalin arzikin Najeriya ke kara bunkasa
- Alhaji Mohammed Idris ya aika muhimmin sako ga kafofin watsa labarai yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaben kasar na shekarar 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Gwamnatin Tarayya ta fito fili ta yi Allah-wadai da iƙirarin da ake yi na cewa ƙasar Najeriya na dab da rugujewa, tana mai jaddada cewa ƙasar ta riga ta hau kan hanyar farfaɗowa.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a jiya Laraba a babban taron shekara-shekara na ƙungiyar kafofin yaɗa labarai ta Najeriya (BON) da aka gudanar a Abuja.

Source: Twitter
Minista ya fadi halin da ake ciki a Najeriya
Ministan ya bayyana cewa, maimakon durƙushewa, Najeriya na nuna juriya a kullum wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da na tattalin arziki, kamar yadda Arise News ta ruwaito.
Ya jaddada cewa gwamnatin Bola Tinubu tana ɗaukar matakai masu tsauri kan tsaro da tattarin arziki, kuma 'yan kasar shaida ne, sun fara ganin yadda kwalliya ke biyan kudin sabulu.
A jawabin nasa, Idris ya bayar da misali da samamen da dakarun soji suka kai a jihohin Zamfara da Niger kwanan nan, inda aka yi nasarar kashe ƴan ta'adda da kuma dakile hare-haren da suka shirya kaiwa.
Ya bayyana cewa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da inganta fannin tattara bayanan sirri sun taimaka ƙwarai wajen rage ƙarfin ƴan ta'adda sassan ƙasar.
Bunkasar tattali da batun masu zuba jari
Game da fannin tattalin arziki, Mohammed Idris ya bayyana cewa alamun nasara sun fara fitowa, inda asusun ajiyar waje na ƙasar ke ƙara ƙarfi, in ji rahoton Vanguard.
Ya kuma ce masu zuba jari daga waje sun sake zuba jari a kasar, wanda ya sa har kamfanonin hada-hadar kuɗi na duniya, FTSE Russell, suka sake mayar da Najeriya a jerin kasashe masu farfadowar tattalin arziki a kwanan nan.
Ministan ya bayyana cewa wannan nasara ta biyo bayan gyare-gyaren da gwamnati ta yi a fannin man fetur da sauran fannoni, waɗanda suka inganta hada hadar kuɗaɗen waje da kuma gaskiya a harkar kasuwanci.

Source: Twitter
Gargaɗi ga kafofin yaɗa labarai
A ƙarshe, Mohammed Idris ya yi kira ga gidajen yaɗa labarai da su kasance masu gaskiya da riƙon amana wajen bayar da rahotanni, musamman yayin da ƙasar ke tunkarar lokacin zaɓe.
Ya yaba wa ƙungiyar BON kan ƙoƙarinta na tabbatar da ƙwarewa a aikin jarida, yana mai jaddada cewa yaɗa labarai na taka rawa sosai wajen kare haɗin kan ƙasa da kuma gina dimuƙuraɗiyya.
Tinubu ya tunkari matsalar tsaro gadan-gadan
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na iya bakin kokarinsa wajen ganin tsaro ya inganta a duka sassan Najeriya.
Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan jim kadan bayan ganawa da Tinubu a gidansa da ke ke Legas.
Ya ce Tinubu na aiki kafada da kafada da hukumomim tsaro da abokan hulda na duniya kamar Amurka da Burtaniya don dawo da tsaro a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

