Najeriya Ta Yi Rashi: Ƴan Ta'adda Sun Hallaka Janar yayin Wani Farmaki
- Ana zargin wani babban jami’in soja, Birgediya-Janar a Najeriya ya rasa ransa bayan harin Boko Haram a jihar Borno
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne yayin da mayaƙa suka kai farmaki da yawa cikin dare
- Rahotanni sun ce sojoji sun kashe mayaƙa da dama a yayin artabun, yayin da jama’a suka bayyana alhini kan rasuwar jami’an tsaro da aka rasa a harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Wani babban jami’in soja, Birgediya Janar O. Braimah ya rasa ransa bayan harin yan Boko Haram a jihar Borno.
Ana zargin an kashe shi bayan harin Boko Haram a Benesheikh, Kaga da ke Borno, a daren Alhamis 9 ga watan Afrilun shekarar 2026 wanda ya tayar da hankali.

Source: Original
Yadda Boko Haram suka kashe janar a Borno
Majiyoyi daga Vanguard sun bayyana cewa mayaƙan sun kai hari da yawa zuwa sansanin sojoji, inda aka gwabza fada mai tsanani tsakanin su da jami’an tsaro da ke wurin.
Wani sakon kafofin sada zumunta daga Mallam Lawan Benesheikh ya bayyana alhini kan babban rashi da Najeriya ta yi yayin yaki da yan ta'adda.
Lawan Benesheikh ya ce:
“Innalillahi wa Inna’illaihin raji’un, Boko Haram ta sake kashe kwamandan Benesheikh.”
Ya kara da cewa harin ya faru ne da daddare lokacin da mayaƙan suka kutsa cikin sansanin sojoji, suna kai farmaki cikin adadi mai yawa.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikansa da gafara ga jaruman da suka rasa rayukansu, yana mai jaddada muhimmancin sadaukarwar da suka yi wajen kare kasa.

Source: Facebook
Shugaban karamar hukumar Kaga ya magantu
A gefe guda, shugaban karamar hukumar Kaga, Hon. Zanna Ajimi, ya tabbatar da faruwar lamarin bayan ziyartar sansanin da aka kaiy harin.
Ya ce:
“Eh, mun bar sansanin yanzu, kuma zan iya tabbatar maka cewa kwamandan yana cikin waɗanda suka mutu a harin.”
Rahotanni sun kuma nuna cewa an kashe wasu daga cikin mayaƙan Boko Haram a yayin arangamar da ta biyo bayan harin, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Halin da mazauna Iran ke ciki bayan sanar da tsagaita wuta tsakanin kasar da Amurka
Ana sa ran karin bayani zai fito daga hukumomin tsaro game da cikakken abin da ya faru da kuma matakan da za a dauka nan gaba.
Wannan ba shi ne karon farko da yan ta'adda ke jawo wa sojojin Najeriya asara yayin da rundunar ke ci gaba da yaki da manyan laifuffuka da ya shafi ta'addanci.
An gwabza tsakanin sojoji, tubabben dan Boko Haram
A baya, an ji cewa wani tsohon ɗan Boko Haram da ya tuba ya samu mummunan sabani da jami'in tsaron sa kai na CJTF a jihar Borno.
Rikici yayi tsanani a lokacin da tubabben dan Boko Haram din ne rike da bindiga kirar AK-47 a hannunsa wanda ya yi arangama da ita.
Mutum guda ya rasa ransa, kuma jami’an tsaro sun kama wanda ake zargi tare da mika shi ga hukuma yayin da ake bincike a birnin Maiduguri.
Asali: Legit.ng
