Nafiu Bala Ya Jagoranci Zanga Zanga zuwa INEC, Ya Mika Bukata kan Kwankwaso da Jagororin ADC
- Shugaban tsagin jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya, Nafiu Bala Gombe, ya jagoranci zanga-zanga zuwa hedkwatar hukumar zabe ta INEC
- Nafiu Bala da magoya bayansa sun bukaci manyan 'yan siyasa da su daina yi musu katsalandan a cikin harkokin jam'iyya
- Zanga-zangar ta samu halartar dan majalisar wakilai na jam'iyyar ADC daga jihar Kogi, Honarabul Leke Abejide
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Masu goyon bayan wani ɓangare na jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin shugabansu, Nafiu Bala Gombe, sun gudanar da zanga-zanga a Abuja.
Masu zangar-zangar karkashin jagorancin Nafiu Bala sun nuna rashin amincewarsu da abin da suka bayyana a matsayin katsalandan ɗin da fitattun ’yan siyasa ke yi a cikin al’amuran jam’iyyar.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa an gudanar da zanga-zangar ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Afirilun 2026.
Magoya bayan ADC sun yi zanga-zanga
Masu zanga-zangar, waɗanda suka riƙe alluna tare da rera taken nuna rashin amincewa, sun buƙaci a bar jam’iyyar ta gudanar da tsare-tsarenta na gida ba tare da matsin lamba daga waje ba.
Masu zanga-zangar sun bayyana sunayen wasu manyan jiga-jigan siyasa, David Mark, Rotimi Amaechi, Atiku Abubakar, Peter Obi, da kuma Rabiu Kwankwaso, inda suka yi kira gare su da su “bar jam’iyyar su huta.”
A cewar ƙungiyar, dole ne ADC ta ci gaba da kasancewa mai zaman kanta, ba tare da tasirin ’yan siyasan da suka yi iƙirarin cewa ba mambobin jam’iyyar ba ne na asali.
Har ila yau, Leke Abejide, ɗan majalisar wakilai na tarayya, ya halarci wannan zanga-zangar domin nuna goyon baya gare su.
Wannan zanga-zanga ta fito da fili irin takun-saƙar da ake yi a cikin gida a jam’iyyar ADC.
Shi dai Nafiu Bala yana iƙirarin shugabancin ADC ne inda yake ta shari’a da ɓangaren da David Mark ke jagoranta a kotu.
Wace bukata Nafiu Bala ya gabatar?
Yayin zanga-zangar ta yau, Nafiu Bala ya buƙaci hukumar INEC da ta amince da shi a matsayin sahihin shugaban ADC, yana mai dogara da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.

Source: Twitter
Ya kuma bayyana cewa ɓangaren David Mark na ƙoƙarin ƙwace ikon jam’iyyar ne ta hanyar da ba ta dace ba, jaridar TheCable ta kawo rahoton.
Idan za a iya tunawa, a ranar 1 ga Afrilu, hukumar INEC ta janye amincewa da shugabancin ADC, inda ta bayyana cewa hakan ya biyo bayan umarnin kotu ne.
Tsohon sanata ya shiga jam'iyyar ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Gaya, ya raba gari da jam'iyyar APC mai mulki.
Sanata Kabiru Gaya ya sanar da sauya shekarsa jam'iyyar ADC bayan ficewa daga APC mai mulki a jihar Kano da Najeriya
Kabiru Gaya ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne bayan natsuwa da shawarwari masu faɗi, inda ya nuna barin APC ya dace da muradun mutanen da yake wakilta da kuma ra'ayinsa na kansa.
Asali: Legit.ng

