Gwamnatin Najeriya Ta Jero Jihohi 10 da za a Yi Ambaliyar Ruwa

Gwamnatin Najeriya Ta Jero Jihohi 10 da za a Yi Ambaliyar Ruwa

  • Gwamnatin tarayya ta fitar da sabon gargadi game da fargabar ambaliyar ruwa a wasu yankuna da dama a jihohin Najeriya har guda 10
  • Hakan na zuwa ne yayin da aka fara samun ruwan sama a jihohin Arewacin Najeriya a baya-bayan nan, alamun da ke nuna damuna ta fara
  • Biyo bayan gargadin, hukumomi sun fitar da matakan da ya kamata mutane su dauka domin kare kan su daga bala'in da zai iya biyo ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa wasu wurare a jihohi 10 na iya fuskantar ruwan sama mai yawa wanda zai iya haddasa ambaliya tsakanin ranar 8 ga Afrilu zuwa 12 ga Afrilu, 2026.

Cibiyar gargadin ambaliya ta kasa karkashin ma’aikatar muhalli ta tarayya ce ta fitar da gargadin domin jama'a su dauki matakin kariya.

Kara karanta wannan

Bayan an kama su da ta'addanci, kotu ta sanar da ƴan Boko Haram 18 makomarsu

Gidajen da ambaliya ta shafa a Borno
Yadda ambaliya ta shafi wasu gidaje a jihar Borno. Hoto: Muhammad Goni
Source: Getty Images

Gargadi kan ambaliya a jihohin Najeriya

Punch ta wallafa cewa an bayyana haka ne a cikin wata sanarwa mai kwanan wata 8 ga Afrilu, 2026, wadda Daraktan sashen kula da zaizayar kasa, ambaliya da yankunan gabar teku, Usman Bokani, ya sanya wa hannu.

“Wadannan wurare da kewayensu na iya fuskantar ruwan sama mai yawa wanda zai iya haifar da ambaliya a cikin wannan lokaci na hasashe: daga 8 ga Afrilu zuwa 12 ga Afrilu, 2026,”

In ji sanarwar.

Jihohin da za a yi ambaliyar ruwa

A cewar ma’aikatar, al’ummomi a jihohin Ebonyi, Anambra, Ogun, Taraba, Cross River, Benue, Imo, Delta, Rivers da Abia na daga cikin wuraren da ake sa ran za su fuskanci ruwan sama mai yawa wanda zai iya haddasa ambaliya a wannan lokaci.

Legit ta rahoto cewa ma’aikatar ta ce a Jihar Ebonyi, Afikpo da Nkalagu na iya fuskantar wannan hadari, yayin da a Jihar Anambra aka lissafo Atani, Iyowa Odekpe, Odekpe da Onitsha.

Kara karanta wannan

Bayan Iran, gwamnatin Trump ta juyo Najeriya, ta yi gargadi kan tsaro

Haka kuma ta ambaci Ayetoro da Ilaro a Jihar Ogun; Donga, Kwata Kanawa, Lau, Serti, Takum da Yorro a Jihar Taraba; da kuma Edor, Ikom da Itigidi a Jihar Cross River.

Sauran wuraren sun hada da Igumale a Jihar Benue; Nworievbi, Okigwe, Otoko da Owerri a Jihar Imo; Oko Anara a Jihar Delta; Port Harcourt a Jihar Rivers; da kuma Umuahia a Jihar Abia.

Taswirar jihar Benue
Taswirar jhar Beneu da ake hasashen ambaliyar ruwa. Hoto: Legit
Source: Original

Ma’aikatar ta jaddada cewa wadannan wurare da kewayensu na iya fuskantar ruwan sama mai yawa wanda zai iya haddasa ambaliya a lokacin da aka kayyade.

Gargadin da gwamnati ta yi

Rahotanni sun nuna cewa hukumar hasashen yanayi ta Najeriya tare da gwamnatin tarayya sun riga sun gargadi manoma da su guji fara noma da wuri sakamakon ruwan sama aka samu a watan Fabrairu da farkon Maris, 2026.

Haka kuma, Gwamnatin Jihar Legas ta bukaci mazauna jihar a watan Maris da su shirya fuskantar ruwan sama mai yawa da ambaliyar gaggawa yayin da damina ke gabatowa.

Legit ta tattauna da Salisu Donga

A wata tattaunwa da wani dan karamar hukumar Donga a jihar Taraba, Salisu Umar Donga, ya bayyana cewa za su yi kokari wajen wayar da kan jama'a.

Kara karanta wannan

Ana batun, tsagaita wuta, Isra'ila ta saba ka'ida, ta hallaka limamin Musulunci

"Tun da mun samu wannan labarin, za mu yi kokari wajen isar da shi ga jama'a domin kaucewa asara.
"Muna fatan gwamnati ma za su yi nasu kokarin."

NiMet ta yi hasashen ruwan sama

A wani labarin, mun kawo muku cewa hukumar hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta bayyana cewa akwai alamun ruwan sama a wasu jihohi.

Hukumar NiMet ta bayyana cewa za a samu ruwan sama a jihohin Gombe, Yobe, Adamawa da wasu yankunan Kudancin Najeriya.

Rahoton hukumar ya yi kira ga jama'a da su kasance cikin shiri tare da daukar matakai masu muhimmanci domin kare rayuwarsu a lokacin ruwan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng