Sheikh Abduljabbar Ya Nemi a Sauya Masa Kurkuku saboda Matsala a Abuja

Sheikh Abduljabbar Ya Nemi a Sauya Masa Kurkuku saboda Matsala a Abuja

  • Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da aka yanke wa hukuncin kisa ya nemi a mayar da shi Kano daga gidan yarin da yake a Abuja
  • Malamin addinin ya bayyana haka ne a wani korafi da ya fitar, inda ya kawo wasu dalilai guda uku game da buƙatar hakan
  • Ana sa ran kotu za ta zauna domin nazari da duba yiwuwar amincewa da bukatar da Sheikh Abduljabbar Kabara ya nema

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da aka yanke wa hukuncin kisa bisa zargin batanci, ya shigar da kara yana neman a mayar da shi Kano daga gidan yarin Kuje a Abuja.

A cikin korafin da ya gabatar a gaban Kotun Daukaka Kara a Kano, mai dauke da kwanan wata 3 ga Afrilu, 2026, malamin ya ce canja masa wuri zuwa Abuja ya hana shi samun muhimman takardun da yake bukata domin daukaka karar da ya shigar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ba Tinubu takobi, ya fadi bangaren da ya ke son ya yaka

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a wajen wa'azi. Hoto: Qadiriyya TV
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa ya bayyana cewa takardun, wadanda suka kunshi sama da shafuka 5,000 da suka kunshi bayanan shari’a da hujjojin da ya ce yana da su, suna gidan yarin Kurmawa lokacin da aka mayar da shi Kuje.

Dalilan neman maido Abduljabbar Kano

Aminiya ta wallafa cewa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya jaddada cewa yana bukatar tabbatar da cikakkun takardunsa kafin a ci gaba da sauraron shari'ar da ake.

Ya ce:

“Yana da muhimmanci na fara tabbatar da cewa takarduna da ke Kurmawa suna nan yadda suke ne kafin a fitar da wata sabuwar sanarwar sauraron kara,”

Bukatunsa uku sun nuna cewa ya bukaci kotu ta ba shi damar komawa Kurmawa domin duba takardunsa, sannan a gyara duk wani abu da ya bata ko aka sauya, tare da dakatar da sauraron karar har sai an tabbatar da cewa takardun suna nan daram.

Abduljabbar zai cigaba da kare kansa

Kara karanta wannan

Ana yakin Iran, Donald Trump ya yi magana kan Kim Jong Un

Malamin ya dage cewa zai kare kansa da kansa a shari’ar daukaka karar, inda ya kafa hujja da sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulki na 1999.

Ya kuma koka cewa duk da yawan zuwan magoya bayansa kotu, har yanzu ba a fitar da takardar da za ta ba shi damar halartar zaman daukaka karar ba.

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara yana wa'azi. Hoto: Qadiriyya TV
Source: UGC

A ranar 15 ga Disamba, 2022, kotun karkashin jagorancin Mai shari’a Ibrahim Sarki-Yola ta same shi da laifi a dukkan tuhume-tuhumen tare da yanke masa hukuncin kisa bisa karar da gwamnatin Jihar Kano ta shigar a kansa.

Malamin addini ya caccaki 'yan siyasa

A wani labarin, mun kawo muku cewa fitaccen malamin Musuluncin nan, Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zariya ya sake wa'azi mai zafi kan shugabannin Najeriya.

Malamin ya koka da cewa ba a yi wa talakawa adalci a fadin Najeriya, inda ya furkata kalmar 'falle' daya da ta karade kafafen sada zumunta.

Alkali Zariya ya ce al'ummar Musulmi da suka kawo gwamnatin Muslim Muslim a zaben shugaban kasar da aka yi a shekarar 2023 ba su ci wata riba ba a mulkinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng