An Ga Tashin Hankali da 'Yan Bindiga Suka Farmaki Tawagar Babban Kwamandan Sojoji
- Dakarun sojojin Najeriya sun fuskanci harin 'yan bindiga a wani yanki na jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma
- Tsagerun 'yan bindigan sun farmaki tawagar kwamanda a rundunar Operation Fansan Yamma lokacin da suke tafiya a karamar hukumar Tsafe
- Dakarun sojojin da ke cikin tawagar sun yi artabu da maharan inda suka samu nasarar tura da dama cikinsu zuwa barzahu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya sun yi arangama da tsagerun 'yan bindiga a jihar Zamfara.
Dakarun sojoji sun kashe ’yan bindiga da dama yayin wata fafatawa da aka yi da tawagar babban jami'i mai kula da shiyya ta 8 (GOC), wanda kuma shi ne kwamandan 'Sector 2' na rundunar Operation Fansan Yamma, a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Sojoji sun yi artabu da 'yan bindiga
A cewar majiyoyi soja ɗaya ne ya riga mu gidan gaskiya a lokacin gumurzun da aka yi da 'yan bindigan.
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Litinin, 6 ga watan Afrilun 2026 yayin da GOC ɗin yake kan hanyarsa ta dawowa daga ziyarar duba dakarun da ke a Kulchin Kalgo da kuma sansanin sojoji da ke Danjibga.
Tawagar sojojin ta yi karo da wasu ’yan ta’adda da ke tserewa, a kauyen Maitashi, wanda hakan ya kai ga musayar wuta.
Dakarun sojoji sun kashe 'yan bindiga
Yayin fafatawar, dakarun sun yi nasarar kashe da dama daga cikin maharan tare da ƙwace makamansu, alburusai, tare da babura.
Duk da haka, soja ɗaya ya samu raunin harbin bindiga, inda aka kai shi cibiyar lafiya ta Keta, inda daga baya aka tabbatar da rasuwarsa.
Dakarun sun kakkabe sauran ɓata-garin daga yankin kafin tawagar ta ci gaba da tafiya zuwa Gusau, yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a yankin a halin yanzu.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga
- Zamfara: Yan bindiga sun kakaba wa kauyuka harajin N16m, sun ba da wa'adin kwanaki
- Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kashe mutane har da sace jami'an tsaro a Sokoto
- Abu ya girma: Na kusa da Gwamna Dauda Lawal ya sha da ƙyar a harin ƴan bindiga
- An rasa babban Sarki: Ƴan bindiga sun bindige basarake yayin hutawa da matarsa
Sojoji sun kashe dan jagoran 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara yayin fafatawa da tsageru, inda suka kashe aƙalla ƴan ta’adda 65 a wani gagarumin samame da suka kai a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Samamen ya yi sanadiyyar mutuwar fitaccen jagoran 'yan bindiga, Kachalla Iliya Sarki, wanda ɗa ne ga babban ɗan ta'adda Ado Aliero dake addabar Arewa maso Yamma.
Baya ga ɗan Ado Aliero, majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an kashe wasu kwamandojin kamar Dogo Sule da Iliya Mai Rasha.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

