Magana Ta Fara Fitowa game da Zargin Gwamnatin Kano da Cefanar da Makarantar FGCK
- Kamfanin gine-gine na Pluck Global ya kare kansa daga cece-kuce kan rabon fili a Kwalejin Tarayya a jihar Kano
- Ya ce yarjejeniyar PPP ta bi duk ka’idoji kuma za a kashe sama da N8bn wajen kammala aikin da aka fara bisa doka
- Kamfanin ya musanta zargin cewa ya haɗa hannu da gwamnatin Kano a shirin karbe filayen makarantar gwamnati a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kamfanin gine-gine na Pluck Global ya fitar da sanarwa domin mayar da martani ga kungiyar tsofaffin daliban kwalejin gwamnatin tarayya (FGCKOSA) kan yarjejeniyar rabon wani yanki na filin makarantar.
A kwanakin nan an taso gwamnatocin Kano da ta tarayya a gaba kan zargin sayar da filin makaranta.

Source: Facebook
Martanin na kunshe a cikin sanarwar da Daraktan gudanarwa na kamfanin, Musaddiq Ado Bala Talle, ya sanya wa hannu a ranar 6 ga Afrilu, 2026, kuma ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan
Abba ya zabi wanda zai zama kwamishinan rikon kwarya bayan tafiyar Hon. Umar Doguwa
Daliban sun a damuwa kan ba da kusan hekta 33 na fili, wanda ya kai kashi 40 cikin 100 na filin makarantar, a karkashin tsarin hadin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP).
Martanin kamfani kan cefanar da filin makarantar Kano
Kamfanin ya bayyana cewa yana da nagartar aiki da bin ka’idoji, inda ya ce wannan yarjejeniya na daga cikin manufofin gwamnatin tarayya na rage gibin kayayyakin more rayuwa.
A cewar kamfanin, ya samu amincewar shiga yarjejeniyar ne tun watan Yunin 2024 domin gyara makarantar baki daya tare da samar da muhimman gine-gine, a madadin wani bangare na filin da ba a amfani da shi yadda ya kamata.
Ya kuma ce an bi dukkannin matakan doka da suka hada da na Hukumar ICRC da kuma kwamitin amincewa da ayyukan ministoci kafin a sahalewa shirin.
Haka kuma, kamfanin ya karyata rade-radin da ke cewa gwamnatin jihar Kano na da hannu a shirin, yana mai cewa filin makarantar ba mallakin gwamnatin jihar ba ne, kuma ba ta taka rawa a ko wane mataki ba.
Yarjejeniyar gwamnati da kamfani kan makarantar FGGC Kano
Pluck Global ya bayyana cewa zai aiwatar da manyan ayyuka ba tare da gwamnatin tarayya ta kashe ko sisi ba a makarantar.
Wadannan sun hada da gina cibiyar koyon sana’o’i, gidajen ma’aikata da dama, dakunan kwanan dalibai mata, cibiyar lafiya, da kuma filin wasanni na zamani.
Sauran ayyukan sun hada da masaukin masu yi wa kasa hidima, dakin taron ma’aikata, gyaran lambun makaranta, da samar da hasken lantarki ta hasken rana.
Haka kuma, za a gyara ajujuwa 54, dakunan gwaje-gwaje na kimiyya, dakin karatu na zamani, da dakunan kwanan dalibai, tare da inganta tsaro da hanyoyin makarantar.

Source: Original
Kamfanin ya ce darajar aikin ya haura N8bn tun a 2024, kuma yanzu darajar na iya ninkuwa saboda halin tattalin arziki. Ya kara da cewa yarjejeniyar PPP ba ta sauyawa bayan an kulla ta.
A karkashin yarjejeniyar, kamfanin zai samu 40% na filin da ba a amfani da shi, yayin da makarantar za ta rike 60% tare da dukkanin gine-ginen da aka inganta.
Kamfanin ya jaddada cewa ba zai karbi filin ba sai bayan kammala aikin gaba daya cikin watanni 36.
Kamfanin ya ce manufar shirin shi ne inganta makarantar da kare martabarta, tare da samar da yanayi mai kyau ga dalibai da malamai, yana mai bayyana cewa yana maraba da tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki
Gwamnan Kano ya yi nadin kwamishina
A baya, mun wallafa cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Dr. Dahir Hashim a matsayin mukaddashin ma'aikatar da Umar Haruna Doguwa ya bari.
Umar Haruna Doguwa, shi ne kwamishinan ma'aikatar ruwa ta jihar Kano kafin ya yi murabus daga mukaminsa domin zama shugaban jam'iyyar APC na Kano.
Sabon kwamishinan rikon wanda matashi ne ya yi alƙawarin inganta samar da ruwa mai tsafta ga al’ummar Kano da suka a dade suna cikin kunci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

