Bayan Hare Haren da Aka Kai a Jihohin Arewa, Tinubu Ya Tunkari Matsalar Tsaro Gadan Gadan
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na iya bakin kokarinsa wajen ganin tsaro ya inganta a duka sassan Najeriya
- Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan jim kadan bayan ganawa da Tinubu a gidansa da ke ke Legas
- Ya ce Tinubu na aiki kafada da kafada da hukumomim tsaro da abokan hulda na duniya kamar Amurka da Burtaniya don dawo da tsaro a Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Gwammatin Najeriya ta jaddada cewa babu abin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fi dauka da muhimmanci kamar tsaro.
Ta ce Shugaba Bola Tinubu na ci gaba da tattaunawa mai zurfi da hukumomin tsaro da abokan hulda domin magance matsalolin tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa a Najeriya.

Source: Twitter
Preminum Times ta tattaro cewa Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan bayan ganawarsa da shugaban kasa a Legas ranar Lahadi.

Kara karanta wannan
Matasa sun dauki mataki mai muni da aka kashe wani bawan Allah kan 'pure water' a Katsina
Tinubu ya dauki matsalar tsaro da muhimmanci
Ya bayyana cewa Babban Kwamandan Askarawan Najeriya ya fi ba da fifiko ga kokarin warware matsalolin tsaro fiye da komai a gwamnatinsa.
A cewar Idris, Tinubu bai jima da zuwa Jos ba, inda al’amuran tsaro suka kasance babban abin da ya mayar da hankali a kai, kuma yana tattaunawa da hukumomin tsaro kan dabarun samar da zaman lafiya mai dorewa.
Wannna na zuwa ne yayin da 'yan ta'adda suka zafafa kai hare-hare a baya-bayan nan, musamman a jihohin Filato, Kaduna, Katsina, Borno, Kebbi da kuma Sakkwato.
Matakan da Shugaba Tinubu ya dauka
Da yake bayanin matakan da Tinubu ya dauka, Mohammed Idris ya ce:
“Ya dawo ne daga Jos, kuma batun tsaro shi ne abu mafi muhimmanci a ran Shugaba Tinubu.
"Yana ci gaba da tattaunawa da hukumomin tsaro kan yadda za mu nemo mafita mai dorewa tare da hadin gwiwa da abokan hulda na kasashen duniya don tabbatar da cewa mun samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.”
Ministan ya jaddada cewa gwamnati ta fahimci cewa matsalar tsaro ta wuce iyakar kasa daya, musamman a yankin Sahel, inda ya jaddada cewa Najeriya ba za ta iya tunkarar wannan kalubale ita kadai ba.
Ya yi nuni da ziyarar da shugaban kasar Chadi, Mahamat Déby, ya kawo Abuja kwanan nan a matsayin wani gagarumin mataki na karfafa hadin gwiwar tsaro a kan iyakoki, cewar The Cable.
“Wannan yana da matukar muhimmanci domin muna yaki da ta’addanci. Ta’addanci ba shi da iyaka, kusan ba zai yiwu Najeriya ta yi hakan ita kadai ba,” in ji shi,

Source: Facebook
Tinubu ya hada kai da Amurka
Ya kara cewa zurfafa hadin gwiwa da kasashe makwabta na da muhimmanci wajen dakile barazanar tsaro a Arewa maso Gabashin Najeriya da kuma yankin Sahel baki daya.
Idris ya kara da cewa shugaban kasar yana kuma aiki kafada da kafada da abokan hulda na kasa da kasa, wadanda suka hada da Amurka, Tarayyar Turai, da kuma Birtaniya, domin karfafa tsarin tsaron Najeriya.
Matakin da aka dauka kan harin Jos
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa harin da aka kai a yankin Angwan Rukuba da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato abin takaici ne matuka.

Kara karanta wannan
Atiku ya gano kura kuran Tinubu a ziyarar jaje da ya kai Filato bayan an kashe bayin Allah
Da yake zantawa da manema labarai, Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce jami’an tsaro sun fara bin sawun wadanda suka kai harin domin kamo su.
Ya ce sojojin Najeriya na ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro da suka hada da sintiri da kuma amfani da bayanan sirri domin gano masu laifi a yankunan da ke cikin hadari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
