Falle 1: Alkali Zariya Ya Sake Caccakar 'Yan Siyasa a Sabon Wa'azin da Ya Yi

Falle 1: Alkali Zariya Ya Sake Caccakar 'Yan Siyasa a Sabon Wa'azin da Ya Yi

  • Malamin Musulunci da ke zaune a jihar Kaduna, Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya caccaki 'yan siyasar Najeriya a wani wa'azi da ya yi
  • Malamin ya koka kan cewa ba a yi wa al'ummar da suka yi tsayuwar daka wajen zaben 'yan siyasa adalci yayin da ya ke fassara wasu ayoyi
  • A kwanakin baya Shugaban majalisar malaman kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya dakatar da Alkali Zariya saboda wani wa'azi da ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Malamin addinin Musulunci, Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zariya ya yi wa'azi domin jawo hankalin 'yan siyasa a Najeriya.

A wa'azin da ya yi, malamin ya ce 'falle daya' wasu 'yan siyasa za su yi, lamarin da ya nuna rashin gamsuwarsa da salon da suke gabatar da wa'azi.

Kara karanta wannan

An kama mai suna 'John' cikin masu kai hari a kungiyar Boko Haram

Alkali Ustaz Abubakar Salihu Zariya
Alkali Salihu Zariya yayin wani wa'azi. Hoto: Alkali Ustaz Abubakar Salihu Zaria
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Alkali Zariya ya yi ne a wani bidiyo da Adda'u Yusuf Sambo ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Maganar Alkali Zariya ga 'yan siyasa

Alkali Abubakar Salihu Zariya ya bayyana cewa an damka amanar tafiyar da rayuwar talakawa a hannun 'yan siyasa masu mulki.

Ya yi tambaya da cewa:

"Akwai amnonin mu a hannun wasu ko babu,"

Muryoyin masu sauraron wa'azin da Alkali Zariya ya yi sun amsa da cewa lallai akwai amanar talakawa a hannun shugabannin Najeriya.

Daga nan kuma sai malamin ya yi kira ga shugabanni da su mika amanar da Allah ya damka musu ga talakawan da suke mulka a kasar nan.

Ya ce:

"Allah ya ce a ba mu kayan mu. A bar mana kayan mu."

Ya kara da cewa Allah ya ce a yi wa mutane adalci ko da mutane sun kasance Musulmi ne, ko Kiristoci, ko 'yan kauye ne ko 'yan birni.

Kara karanta wannan

Babban malami, Sheikh Isah Bauchi ya rasu, Bala Lau ya yi ta'aziyya

Alkali Zariya ya ce falle 1 ce

Malamin ya nuna cewa ba a yi wa mutane adalci a Najeriya duk da fafutukar da al'umma suka yi wajen zaben shugabanni a 2023.

Ya ce:

"Tsakanin ku da Allah ana mana adalci a cikin wannan kasar?'

Bayan tambayar da malamin ya yi, masu sauraron Alkali Zariya sun bayar da amsa da cewa ba a musu adalci a kasar nan

Daga nan sai ya ce:

"In Allah ya yarda falle daya ce. In shaa Allah falle daya ce."

Alkali Zariya ya bayyana cewa ko gwamnatin Muslim Muslim da ta ci gajiyar addinin Musulunci ba ta musu abin da ya kamata.

Ya ce:

"Asali ma muƙamin da ake takama da shi, tsakanin ku da Allah da Musulunci aka ci gajiyarsa ko da kafurci?"

Bayan bayar da masa, malamin ya kara da cewa:

"In shaa Allah falle daya ce."
Sheikh Alkali Salihu Zariya
Alkali Abubakar Salihu Zariya a wajen wa'azi. Hoto: Alkali Ustaz Abubakar Salihu Zaria
Source: Facebook

An dakatar da Alkali Zariya

A wani labarin, mun kawo muku cewa a watan Ramadan da ya gabata, kungiyar Izala ta dakatar da Sheikh Alkali Salihu Zariya daga tafsiri.

Kara karanta wannan

"Najeriya za ta kama da wuta," Timi Frank ya fito da kuskuren INEC gabanin 2027

Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir da ke jagorancin majalisar malaman kungiyar ne ya dauki matakin bayan wani zama a Jos.

Lamarin ya biyo bayan wani wa'azi mai zafi da Alkali Salihu Zariya ya yi game da 'yan siyasa a wajen da ya ke gabatar da tafsiri a jihar Yobe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng