Ministan Buhari Ya Jingina Zalunci ga Shugaban INEC, Ya Tona Badakalar da aka Yi a Jami'a

Ministan Buhari Ya Jingina Zalunci ga Shugaban INEC, Ya Tona Badakalar da aka Yi a Jami'a

  • Tsohon ministan matasada wasanni, Solomon Dalung, ya zargi shugaban INEC da rashin gaskiya tun ba yanzu ba
  • Dalung ya danganta zargin da abubuwan da suka faru a Jami’ar Jos lokacin da Joash Amupitan yake shugaba sashen shari’a
  • Ya ce gargadin da aka yi wa ADC ba ya da tushe, kuma an yi shi ne domin razana ‘yan adawa ba wai don ana kan gaskiya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya soki shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, inda ya ce ba shi da gaskiya ko kadan.

Dalung ya bayyana cewa Amupitan bai cancanci yin tsokaci kan harkokin siyasa ba, musamman dangane da gargadin da aka ce ya yi wa jam’iyyar ADC.

Kara karanta wannan

Rashin taya Trump yaki da Iran ya harzuƙa shi, ya ci mutuncin Shugaban Faransa da matarsa

Dalung ya yi tir da Amupitan ya kwatanta ADC da abin da ya faru a Zamfara
Joash Amupitan, shugaban INEC a yayin wani taro, alamar jam'iyyar ADC Hoto: INEC Nigeria/ADC Party
Source: Twitter

A hira da ya yi da Trust TV, ya ce ya san Amupitan tun daga shekarar 1991 lokacin da yake dalibi, sannan daga baya suka yi aiki tare a jami’a a 2004.

Shugaban INEC ba shi da gaskiya – Darlung

Sahara Reporters ta wallafa Dalung ya kara da cewa akwai abubuwan da suka faru a lokacin da Amupitan yake shugaba a sashen shari’a a jami’ar Jos, wanda a cewarsa ya nuna ba shi da mutunci.

Ya ce:

“Mutumin da na sani ba shi da gaskiya, don haka ba zan tsaya in kare shi ba.”

Dalung ya kuma soki gargadin da aka danganta ga shugaban INEC kan ADC, yana mai cewa hakan wata hanya ce ta tsoratar da ‘yan adawa.

Dalung da ya yi Minista a zamanin Muhammadu Buhari ya tambaya ko Amupitan ya fahimci ainihin abin da ya faru a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Rigima sabuwa: Trump ya jefawa mataimakinsa zargi kan yakin Iran

Ya bayyana cewa rikicin da aka samu a can ba ya da alaka da shugabancin jam’iyya, illa dai rashin bin ka’idojin zabe wajen fitar da ‘yan takara

Dalung ya soki Amupitan a kan ADC

Dalung ya yi ikirarin cewa a lokacin da Amupitan yake shugaban sashen shari’a a jami’ar Jos, an samu danniya a sakamakon dalibai.

Solomon Dalung ya ce Amupitan ba mai gaskiya ba ne
Solomon Dalung, tsohon minista a yayin wani taron manema labarai Hoto: Solomon Dalung
Source: Getty Images

Ya ce a shekarar karatu ta 2009 zuwa 2010, an sauya sakamakon dalibai 16 da suka samu sakamakon 2-1.

Sai aka ba wa dalibai na musamman, ciki har da jami’an ‘yan sanda da ‘yan siyasa, suka samu irin wannan sakamako duk da cewa ba sa halartar karatu yadda ya kamata.

Dalung ya ce shi ne ya jagoranci fafutukar neman adalci ga daliban, duk da barazanar da aka yi masa cewa ba zai kammala karatun digirinsa na biyu ba idan bai janye ba.

A cewarsa, daga cikin daliban, an samu nasarar mayar wa guda takwas hakkinsu, yayin da biyu suka rasa shi har abada.

Ya kara da cewa shi ma ya fuskanci matsaloli sakamakon wannan fafutuka, inda aka jinkirta fitar da sakamakonsa na tsawon shekaru biyu.

Kara karanta wannan

Matashin da aka kama a Najeriya kan yakin Iran da Amurka ya fadi masu hannu a tsare shi

Dalung ya jaddada cewa har yanzu akwai karin zarge-zarge kan batun, yana mai cewa daliban da abin ya shafa suna nan da rai.

ADC ta fallasa shirin INEC

A wani labarin, mun wallafa cewa ADC mai adawa a Najeriya ta nuna damuwa kan abubuwan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) take yi mata.

Jam'iyyar ADC ta yi zargin cewa hukumar zabe ta INEC na shirin kawo mata cikas a zaben shekarar 2027 da ake tunkara Bayan ta doke shugabanninta na ƙasa.

Kakakin jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya kara da bayyana cewa INEC ta dana wa jamiyyarsu tarkon da zai sanya ta kasa gabatar da 'yan takara a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng