Yadda aka Kashe Budurwa da Harbin Bindiga Tana Shirin Tafiya Aure a Borno

Yadda aka Kashe Budurwa da Harbin Bindiga Tana Shirin Tafiya Aure a Borno

  • Rahotanni sun nuna cewa harbin bindiga ya samu wata budurwa a birnin Maiduguri na jihar Borno kuma ta rasu jim kadan bayan lamarin
  • Mutuwar budurwar ya dauki hankalin al'umma a fadin Najeriya kasancewar harsashin ya same ta ne a lokacin da ta ke zaune a cikin gidansu
  • Kungiyar Amnesty International da ke rajin kare hakkin dan Adam ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta gaggauta bincike domin daukar mataki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - An kashe wata budurwa mai shekaru 14 sakamakon harbin bindiga da aka harba a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 4 ga Afrilu, lokacin da aka ce harbi ya samu wata dalibar makarantar sakandare a lokacin da ta ke cikin gidansu da ke rukunin gidaje na asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH).

Kara karanta wannan

Bana ka taba: Faransa ta tura sojoji da tankokin yaki domin a yaki Isra'ila

Budurwar da aka kashe a Borno
Budurwar da ta mutu sakamakon harbin bindiga a Borno. Hoto: Amnesty International
Source: Facebook

A bayanin da Amnesty International ta yi a Facebook, ta ce an harba harsashin da ya kashe ta ne sakamakon harbin bindiga yayin murna a wani bikin aure da ake a kusa da su.

Wane ne ya kashe budurwa a Borno?

Yayin da ake zargin wani soja ne ya harba harsashin, wani sako da aka ga Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa wata majiya ta daura laifin kan kungiyar Civilian Joint Task Force (CJTF).

Majiyar ta ce:

“An ce jami'in CJTF ne, ba jami’an soja ba ke da alhakin harsashin da ya kashe budurwa mai shekaru 14 a yankin Costain na Maiduguri, a cewar Operation Hadin Kai.
“Rundunar ta ce binciken farko ya nuna cewa wasu mambobin CJTF na harba bindiga ne yayin wani taro a wani gida da ke kusa da su a lokacin da lamarin ya faru.
“An bayyana wannan aiki a matsayin wanda ba a amince da shi ba da kuma rashin kwarewa, inda hukumomi suka fara bincike domin gano masu hannu a ciki da kuma hana sake faruwar hakan.

Kara karanta wannan

Rikicin Jos ya rutsa da Ibrahim, an kashe matashi ɗan NYSC daga yin aurensa

"Operation Hadin Kai ta kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayiyar tare da rokon jama’a da su guji yada bayanan da ba a tantance ba,”
Taswirar jihar Borno
Taswirar jihar Borno a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Yadda aka kashe budurwa a Borno

Wani abokin 'yan uwar budurwar ya bayyana yadda lamarin ya faru, yana cewa mintunan karshe na rayuwarta sun kasance cike da farin ciki, tana shirin zuwa wani biki.

“Ta na zaune ne da 'yan uwanta a rukunin gidajen UMTH, kuma tana cikin gida lokacin da wannan ibtila’i ya faru.
"Ta gama sanya lalle ga mahaifiyarta, tana cikin farin ciki tana shirin halartar bikin auren da aka shirya a ranar,”

Inji majiyar.

Kungiyar Amnesty ta yi Allah wadai da lamarin, tana bukatar a gaggauta bincike domin daukar mataka da suka dace wajen yi mata adalci.

An kama 'Johh' cikin 'yan Boko Haram

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an tsaron Najeriya sun kama wasu mutane uku da suka amsa cewa su 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Daya daga cikin mutanen da aka kama ya sanar da cewa sunan shi John Audu kuma yana cikin 'yan kungiyar Boko Haram a lokacin.

John ya sanar da cewa a lokacin da aka kama su sun fara shirin kai hari wani barikin sojoji da ke karamar hukumar Mubi a jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng