Abba Kabir Ya Magantu kan Tasirin APC a Kano, Ya Yi wa Tinubu Babban Alƙawari

Abba Kabir Ya Magantu kan Tasirin APC a Kano, Ya Yi wa Tinubu Babban Alƙawari

  • Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kwarara yabo ga Shugaba Bola Tinubu game da jagorancin da yake yi a Najeriya
  • Abba Kabir ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai ƙoƙari, yana roƙon al’ummar Kano su mara masa baya a 2027
  • Yusuf ya ce shugaban ƙasa ya inganta tattalin arziki tare da faɗaɗa ayyukan more rayuwa duk da ƙarancin kuɗin gwamnati, yana nuna jajircewa wajen gina ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana tasirin da jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ke da shi a jihar Kano.

Abba Kabir ya bayyana cewa Bola Tinubu shugaba ne mai ƙoƙari wanda ke samar da ribar dimokuraɗiyya a faɗin ƙasa ga jama’a.

Abba Kabir ya yi wa Tinubu alkawarin nasara a Kano
Gwamna Abba Kabir da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Abba ya fadi abubuwan da Tinubu ya yi

Kara karanta wannan

Yadda Iran ta riƙa kakkaɓo jiragen 'maƙiya' daga sararin samaniyarta

Hakan na ciki wani jawabi ga taron jama’a a gidan gwamnatin Kano bayan dawowa daga taro a Abuja, cewar rahoton Vanguard.

Abba Kabir Yusuf ya ce Tinubu ya samu ci gaba wajen ƙarfafa tattalin arziki da bunƙasa manyan ayyukan more rayuwa.

Ya ce:

“Shugaban ƙasa yana yin iya ƙoƙarinsa domin wannan ƙasa, ya ƙarfafa tattalin arziki kuma yana tabbatar da ayyukan more rayuwa sun kai kowane yanki.”

Abba Kabir ya yaba da jajicewar Tinubu a Najeriya

Abba Kabir Yusuf ya gode wa Tinubu bisa jajircewarsa wajen kare dimokuraɗiyya da gina ƙasa, yana ƙara da cewa al’ummar Kano suna cikakken goyon baya ga shugaban ƙasa.

“Mutanen Kano suna tare da shugaban ƙasa, kuma za mu goyi bayan sake zaɓensa a 2027, da yardar Allah.”

- Abba Kabir Yusuf

Abba Kabir ya yaba wa Tinubu kan abin alheri
Gwamna Abba Kabir Yusuf yana jawabi a taro. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

'Karfin da APC ke da shi a Kano'

Gwamnan ya kuma jaddada ƙarfin jam’iyyar APC mai mulki a Kano, yana mai cewa ita ce kaɗai jam’iyya mai nasarar lashe zaɓe a duk matakai.

Ya ce babu wata jam’iyya da za ta iya karɓe iko a Kano ko Najeriya, yana yaba nasarorin taron yankin Arewa maso Yamma da babban taron jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Jagora a APC, Danbilki Kwamanda ya fadi wanda zai ci zaben Kano a 2027

Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da saka jari a fannoni kamar ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, noma, samar da ayyukan yi da ƙarfafa mata da matasa.

Hakan na zuwa bayan Gwamna Abba Kabir ya yi murabus daga jam'iyya NNPP inda daga bisani ya shiga APC mai mulkin Najeriya, cewar rahoton Punch.

Abba, Ganduje sun gana kan mataimakin gwamna

Mun ba ku labarin cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da tsohon Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje sun sa labule game da kujerar mataimakin gwamna.

Jagororin biyu sun yi wata ganawar sirri a Abuja kan rikicin siyasar Kano da ke sauya salo kuma tana ɗaukar zafi yayin da ake shirin zaben shekarar 2027.

Tattaunawar ta shafi sauya sheƙa da ake sama jihar, musamman bayan Nasiru Yusuf Gawuna ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC da yan adawa suka dauke ta a matsayin dandalin siyasa a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.