Dr Bashir Aliyu Ya Yi Gargadi kan Sabon Tsarin INEC ana Shirin Zaben 2027

Dr Bashir Aliyu Ya Yi Gargadi kan Sabon Tsarin INEC ana Shirin Zaben 2027

  • Malamin addinin Musulunci, Dr Bashir Aliyu Umar ya gargadi hukumar INEC kan kawo sabon tsarin tantance masu zabe kafin siyasar 2027
  • Malamin ya bayyana cewa kawo tsarin a daidai lokacin da aka fara fuskantar zabe zai kawo cikas ga masu kada kuri'a musamman a Arewa
  • A ranar Juma'a hukumar INEC ta sanar da cewa za ta fara tantance jaristar masu kada kuri'a da suka yanki katin zabe tsakanin 2011 zuwa 2024

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Babban limamin masallacin Al-Furqan da ke Kano, Dr Bashir Aliyu Umar, ya soki hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan umarnin da ta bayar cewa dole ne a sake tantance duk masu zaɓe.

Malamin, wanda kuma shi ne shugaban majalisar koli ta shari’a a Najeriya (SCSN), ya yi wannan gargadi ne yayin hudubar Juma’a da ya gabatar a Kano.

Kara karanta wannan

Ana maganar 2027, INEC ta kawo sabon tsari da dole mai zabe ya bi

Dr Bashir Aliyu Umar da Joash Amupitan
Dr Bashir Aliyu a hagu, shugaban INEC, Joash Amupitan a dama. Hoto: INEC Nigeria|Dr Bashir Aliyu Umar
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Dr Bashir Aliyu Umar ya yi game da hukumar INEC ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Gargadin Dr Bashir ga INEC

Dr Bashir Aliyu ya bayyana shirin tantance masu zabe a matsayin rashin adalci, yana mai gargadin cewa zai iya hana miliyoyin ‘yan Najeriya haƙƙinsu na kaɗa ƙuri’a, musamman ma waɗanda ke zaune a karkara.

Ya ce dokar zaɓe ba ta tanadi sake tantance masu kada kuri'a ba, tare da tambayar yadda za a kammala irin wannan aiki cikin ƙasa da watanni biyu.

Malamin ya kara da cewa duk wanda ke da katin zaɓe yana da haƙƙin zaɓe domin yanke hukuncin kan wanda zai mulke shi.

Ya yi zargin cewa INEC na ƙoƙarin mayar da katin zaɓe maras amfani duk da cewa an ɗauki lokaci mai tsawo ana wayar da kan jama’a kan muhimmancinsa.

Kara karanta wannan

An je gidan malamin Musulunci da zai nemi gwamna za a kashe shi

Kalubale kan sabon tsarin INEC

Daily Trust ta rahoto malamin ya yi gargadin cewa wannan tsari na iya haifar da rikici idan ‘yan ƙasa suka ga ana tauye musu haƙƙinsu.

Ya kwatanta hakan da irin zanga-zanga da rashin zaman lafiya da aka gani a ƙasashe kamar Libya, Sudan da Syria, yana kira ga shugabannin Najeriya da su guji ɗaukar matakan da za su iya janyo irin wannan rikici.

Yadda aka yi zabe a Abuja
Wani matashi na kada kuri'a a zaben da aka yi a Abuja. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Neman sauke shugaban INEC

Dr Bashir ya sake jaddada kiran da ya yi na a cire shugaban INEC daga mukaminsa, yana zargin shugaban hukumar da ɗauke da mugun nufi ga Musulman Najeriya.

Ya ce gajeren lokacin da aka bayar don sake tantance katunan ba zai yiwu ba, yana mai zargin cewa an shirya shi ne domin rage yawan masu kaɗa ƙuri’a.

A karshe, ya yi kira ga ‘yan majalisar dokoki su ƙi amincewa da sabon tsarin INEC, yana cewa al'umma na jiran su domin ba a ji komai daga gare su ba.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shugaban Amurka, Trump ya 'kori' Antoni Janar ana tsaka da yakin Iran

Ga bidiyon Dr Bashir da Premier Radio ta wallafa a X.

Temi Frank ya gargadi INEC

A wani labarin, kun ji cewa tsohon jigo a jam'iyyar APC, Temi Frank ya gargadi hukumar INEC kan goge sunayen shugabannin ADC a shafinta.

Ya bayyana cewa matakin da hukumar ta dauka zai iya jawo babban rikici a Najeriya kamar yadda aka samu irin haka a wasu kasashe.

Hukumar INEC ta sanar da cewa matakin da ta dauka kan goge sunayen shugabannin ADC ne saboda karar da wani dan jam'iyyar ya shigar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng