Ana Maganar 2027, INEC Ta Kawo Sabon Tsari da Dole Mai Zabe Ya Bi
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kawo sabon tsari ga masu kada kuri'a yayin da ake cigaba da shirye-shiryen zaben 2027
- Rahotanni sun nuna cewa shirin ya shafi yadda za a tantance masu zabe da suka riga suka yi rajista da hukumar INEC a shekarun baya
- INEC ta bayyana lokuta da ranakun da kowane dan kasa da ya yi rajista zai je ofishinta domin a tantance bayanan shi ko ta yanar gizo
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da shirin fara tantance rijistar masu zaɓe a faɗin ƙasar nan, domin cire sunayen waɗanda ba su cancanta ba da kuma ƙarfafa sahihancin tsarin zaɓe a Najeriya.
Hakan na zuwa ne yayin da 'yan kasa da jam'iyyun siyasa suka fara shirye-shiryen tunkarar zaben Najeriya da za a yi a shekara mai kamawa.

Source: Facebook
Dalilin tantance masu zabe
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma’a, hukumar ta ce za a cire wadanda ba su cancanta ba kamar matattu, waɗanda ba ‘yan Najeriya ba, yara ƙanana, da masu rajista fiye da sau ɗaya.
Hukumar INEC ta bayyana cewa aikin ba sabon rajista ba ne, kuma zai shafi waɗanda suka yi rajista tsakanin shekarar 2011 zuwa 2024 ne kawai.
Sanarwar ta ce:
“Wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin hukumar na sabuntawa, tsaftacewa da ƙarfafa sahihanci, inganci, da amincin rijistar masu zaɓe na ƙasa gabanin zaɓe mai zuwa.”
Yadda INEC za ta tantance masu zabe
Jaridar Punch ta rahoto cewa hukumar ta ce za a gudanar da aikin ta hanyar yanar gizo da kuma a cibiyoyin da aka ware a faɗin ƙasa.
INEC ta fitar da jadawalin matakai, inda za a fara daga ranar 13 ga Afrilu zuwa 29 ga Mayu, 2026, a matakan ƙananan hukumomi, yankunan rajista da rumfunan zaɓe.
Za a rika gudanar da aikin daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana a kowace rana, ciki har da ƙarshen mako da ranakun hutu.
Ga masu yin ta ta yanar gizo, hukumar ta bukaci su shiga shafinta domin ƙirƙirar asusu tare da shigar da lambar katin zaɓensu ko bayanan su don tantancewa.
“Aikin zai yi amfani da hoton fuska wajen tabbatar da mutum, sannan za a tantance bayanan da ke cikin babban kundin rijistar masu zaɓe,”
Inji INEC

Source: Facebook
Ga waɗanda za su je ofishin INEC da kansu, ana buƙatar su kai bayanan katin zaɓensu zuwa cibiyoyin hukumar inda jami’ai za su tantance su tare da sabunta duk wani bayani da ya dace.
INEC ta goge sunayen manyan ADC
A wani labarin, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta dakatar da hulda da jam'iyyar adawa ta ADC har sai bayan hukuncin kotu.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan ya sanar da cewa sun dauki matakin ne sakamakon wani dan jam'iyyar da ya shigar da kara.
Saboda halin da ake ciki, INEC ta goge sunayen manyan jam'iyyar daga shafinta, ciki har da shugaban ADC, Sanata David Mark da sauransu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

