Yakin Iran Ya Ki Karewa, Najeriya, Kasashe 39 Sun Yi Zama Domin Shawo kan Lamarin
- Kasashe 40 ciki har da Najeriya sun gudanar da taro domin nemo hanyoyin dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin Hormuz
- Hakan ya biyo bayan matakin rufe mashigar da Iran ta yi dalilin yakin da ake yi tsakanin ta da Isra'ila da Amurka
- Barazanar hare-haren Iran da ramuwar gayya ta dakatar da zirga-zirga a mashigar, lamarin da ya jawo tashin farashin mai a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Yayin da matsin lamba ke karuwa kan rufe mashigar Hormuz da Iran ta yi, kasashe 40 ciki har da Najeriya sun yi taron gaggawa.
Ƙasashen sun yi taron yanar gizo domin nemo mafita musamman saboda rufe mashigar Hormuz da ya taba arzikin duniya.

Source: Facebook
An shirya taron ne bisa bukatar Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, bayan shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar janyewa daga kungiyar NATO saboda rikicin, cewar Reuters.
Yadda hare-hare ke jawo matsala a mashigar Hormuz
Hare-haren ramuwar gayya da Iran ke kai wa jiragen kasuwanci sun kusa dakatar da duk wata zirga-zirga a mashigin, wanda ke hada tekun Gulf da sauran tekunan duniya.
Wannan lamari ya katse muhimmin hanyar safarar mai a duniya, lamarin da ya jawo tashin gwauron zabi a farashin man fetur a kasuwannin duniya.
Kasashe kamar Birtaniya, Faransa, Jamus, Italiya, Canada, Japan da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bukaci Iran ta daina toshe mashigar Hormuz.
Sun kuma yi alkawarin bada gudunmawa wajen tabbatar da tsaro da zirga-zirga cikin lumana a wannan muhimmiyar hanyar ruwa ta duniya.
Ministar harkokin wajen Birtaniya, Yvette Cooper, ta soki halin Iran tana mai cewa yana barazana ga tsaron tattalin arzikin duniya baki daya.
Ta ce an kai hare-hare sama da 25 kan jiragen ruwa, yayin da ma’aikatan ruwa kusan 20,000 suka makale a kan jirage sama da 2,000, cewar rahoton Vanguard.
Ta kara da cewa ana hada masu tsara harkokin soja domin nazarin yadda za a kawar da bama-bamai a mashigin domin dawo da tsaro.

Source: Getty Images
Abin da Firayim ministan Birtaniya ya ce
Firaminista Starmer ya ce dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa ba zai zama abu mai sauki ba sai da hadin gwiwar soja da diflomasiyya.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce amfani da karfi ba zai yiwu ba, yana mai cewa dole a yi aiki da Iran bayan tsagaita wuta.
Kungiyar kasashen Gulf ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta ba da izinin amfani da karfi domin kare mashigar daga hare-haren Iran.
Sai dai wannan kuduri ya raba kan kasashe mambobi, inda Rasha, China da Faransa suka nuna adawa da matakin.
A halin yanzu Iran na shirin kulla yarjejeniya da Oman domin sa ido kan zirga-zirga a mashigin Hormuz.
Iran ta yi barazana ga Amurka da Isra'ila
Mun ba ku labarin cewa dakarun 'Islamic Revolutionary Guard Corps' a Iran watau IRGC ta yi gagarumar barazana ga Amurka da Isra'ila a yakin da ake yi.
IRGC ta yi barazanar kai hari kan jami’o’in Amurka a Gabas ta Tsakiya bayan hare-haren da suka lalata wasu jami’o’i a Iran.
Ta bukaci Amurka ta yi Allah-wadai da harin kafin wa’adin da aka sanya, tare da gargadin ma’aikata da dalibai su guji kusantar harabar jami’o’i.
Asali: Legit.ng


