Atiku Ya Gano Kura Kuran Tinubu a Ziyarar Jaje da Ya Kai Filato bayan an Kashe Bayin Allah
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zargi Bola Ahmed Tinubu da rashin kusantar jama’a yayin ziyararsa a Filato
- Ya ce shugaban bai ziyarci wuraren da aka kai hare-hare ko asibitoci ba, amma ya takaita ga wuri daya da bai kamata ba
- Atiku ya kuma soki yadda aka mayar da ziyarar tamkar siyasa maimakon jajantawa ga mutanen da suka rasa ƴan uwansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau –Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan ziyarar da ya kai jihar Filato.
Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa Tinubu bai gana kai tsaye da wadanda rikicin ya shafa ba ko zuwa wuraren da lamarin ya faru ba.

Source: Twitter
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Phrank Shaibu, ya fitar.
Atiku ya soki ziyarar Tinubu a Filato
Jaridar Punch ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya bayyana ziyarar a matsayin alama mai tayar da hankali, inda Shugaban kasan ya yi baya-baya da halin da jama’a ke ciki.
Ya ce abin mamaki ne kuma mai tayar da hankali yadda kwanaki bayan kashe-kashen fararen hula, ziyarar shugaban ba ta wuce gefen jirginsa a filin jirgin sama ba.
A cewarsa, shugaban bai kai ziyara wuraren da aka kai hare-haren ba, haka kuma bai gana da iyalan da suka rasa ‘yan uwansu ko wadanda ke kwance a asibitoci ba.
Tinubu na sauri ya wuce Legas – Atiku
Atiku Abubakar ya yi zargin cewa an takaita ziyarar cikin gaggawa domin shugaban ya wuce Legas domin hutun Easter, lamarin da ya ce yana nuna rashin fifita abin da ya dace a lokacin da kasa ke cikin jimami.

Kara karanta wannan
Tinubu zai ziyarci jihohi 4, zai fara da Jos inda aka kashe Musulmai da Kiristoci
Ya ce:
“A lokacin da iyalai ke cikin alhini, an takaita ziyarar zuwa tsayawa na dan lokaci a gefen jirgin sama, nesa da wadanda abin ya shafa ke ciki.”
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma soki abin da ya kira mayar da ziyarar ta zama harkar siyasa.
Ya yi zargin cewa shugaba Tinubu ya gana da magoya bayan jam’iyya a Jos maimakon ganawa da wadanda rikicin ya shafa.

Source: Facebook
Ya ce:
“Wannan ba shugabanci ba ne; sakaci ne da aka lullube da tsarin aiki.”
Ya kara da cewa:
“Maimaita irin wannan abu ba kuskure ba ne kawai, ya zama dabi’a mai tayar da hankali.”
Haka kuma, ya ce babu wata sabuwar manufa ko matakin tsaro mai karfi da aka sanar yayin ziyarar Filato, abin da ke jefa shakku kan yadda gwamnati ke tunkarar matsalar tsaro.
Matakan da Tinubu ya dauka kan Filato
A baya, mun wallafa cewa hare-haren 'yan bindiga sun jawo asarar rayukan bayin Allah da dama a jihar Filato da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya a ƙarshen makon da ya wuce.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara zuwa birnin Jos na jihar Filato domin jajantawa kan mummunan lamarin da ya faru a Rukuba, wanda ya jawo wasu rikice-rikicen.
Bayan ya sauka a jihar, Shugaban kasar ya bayar da umarni ha hafsoshin tsaro umarnin su gaggauta zakulo bata garin da suka aikata wannan danyen aikin domin su fuskanci hukunci.
Asali: Legit.ng

