Matakai 2 da Tinubu Ya Dauka bayan Ya Je Ziyarar Jaje a Plateau

Matakai 2 da Tinubu Ya Dauka bayan Ya Je Ziyarar Jaje a Plateau

  • Hare-haren 'yan bindiga sun jawo asarar rayuka a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara zuwa birnin Jos na jihar Plateau domin jajantawa kan mummunan lamarin da ya faru
  • Mai girma Bola Tinubu ya ba hafsoshin tsaro umarnin su gaggauta zakulo bata garin da suka aikata wannan danyen aikin

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarni kan kisan gillar da 'yan bindiga suka yi a jihar Plateau.

Shugaba Tinubu ya umarci hafsoshin tsaro da Ministan tsaro da su kamo waɗanda suka kashe mutane a Plateau, sannan su gaggauta ƙarfafa matakan tsaro a jihar domin magance hare-haren da ke yawan faruwa.

Shugaba Tinubu ya kai ziyara jihar Plateau
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce Shugaba Tinubu ya bayar da wannan umarnin ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Afirilun 2026 yayin da yake jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki a birnin Jos.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Na kusa da Gwamna Dauda Lawal ya sha da ƙyar a harin ƴan bindiga

Tinubu ya kuma sanar da cewa gwamnatin tarayya za ta tura na’urorin CCTV guda 5,000 zuwa Jihar Plateau domin taimakawa wajen tattara bayanan sirri, sa ido, da kuma kai dauki cikin sauri ga duk wata barazanar tsaro.

Tinubu ya yi Allah wadai da harin Plateau

Wannan umarni na zuwa ne daidai lokacin da Shugaban ya isa Jos domin jajantawa gwamnati da al’ummar jihar kan harin da wasu ’yan bindiga suka kai a Angwan Rukuba, Jos ta Arewa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 28.

Yayin da yake Allah-wadai da harin, Tinubu ya ce ba a zaɓe shi domin ya mayar da mata da maza zawarawa ba, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Gwamna Mutfwang ya yi jawabi

Tun farko a jawabinsa, Gwamna Mutfwang ya tarbi shugaban ƙasa, inda ya bayyana cewa ziyarar tasa ta zo ne a daidai lokacin da jihar ke jin daɗin kwanciyar hankali tare da jan hankalin masu zuba jari na gida da na waje kafin faruwar lamarin na ranar Lahadi.

Mutfwang ya ce harin wani babban koma-baya ne na ɗan lokaci, amma ya nuna kwarin gwiwar cewa, tare da goyon bayan gwamnatin tarayya da jami’an tsaro, jihar za ta shawo kan wannan ƙalubale.

Kara karanta wannan

Bayan ministoci sun yi murabus, Tinubu ya yi sababbin nade nade a Najeriya

Shugaba Tinubu ya umarci a kamo masu kai hari a Plateau
Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasar Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Muftwang ya yaba wa hukumomin tsaro

Ya yaba wa jajircewar hukumomin tsaro, waɗanda suke dakatar da hare-hare da dama ba tare da jama’a sun sani ba, sannan ya bayyana cewa ya kira taron majalisar tsaro inda aka yanke muhimman shawarwari.

Gwamnan ya tuna cewa matsalar tsaro ta daɗe tana addabar jihar kusan shekaru 30, tun daga zamanin tsofaffin gwamnoni Joshua Dariye, Sanata Jonah Jang, da Simon Lalong, amma ya lura cewa jagorancin Shugaba Tinubu ya samar da sabon babi na haɗin kai tsakanin shugabannin Plateau.

''Mun shiga tashin hankali'

Wata mazauniyar Jos, Maryam Isma'il, ta bayyana cewa sun shiga tashin hankali sakamakon lamarin.

"Lamarin ya faru ne a kusa da unguwarmu kuma mun shiga tashin hankali sosai sakamakon kashe-kashen. Mun ji tsoron cewa wani sabon rikici na iya barkewa."
"Ya kamata gwamnati ta dauki matakan da suka dace domin kawo karshen kisan da ake yi wa jama'a ba gaira ba dalili."

Kara karanta wannan

2027: Jerin ministoci da manyan jami’an gwamnatin Tinubu 7 da suka yi murabus don takara

- Maryam Isma'il

Tinubu ya yi sababbin nade-nade

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sababbin nade-nade a gwamnatinsa.

Shugaba Tinubu ya amince da nadin Dalhatu Abubakar a matsayin shugaban hukumar kula da kasuwancin kasa, NCX.

Tinubu ya nada Sanata Ibrahim Ida a matsayin wanda zai sa ido a aikin hukumar CAC domin inganta harkokin kasuwanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng