An Rasa Babban Sarki: Ƴan Bindiga Sun Bindige Basarake yayin Hutawa da Matarsa

An Rasa Babban Sarki: Ƴan Bindiga Sun Bindige Basarake yayin Hutawa da Matarsa

  • Wasu ‘yan bindiga sun kashe babban basarake bayan sun kai hari gidansa da dare, lamarin da ya girgiza al’umma
  • Rahotanni sun ce maharan sun harbe shi ta taga yayin da yake hutawa da matarsa a jihar Ebonyi
  • Shugabar karamar hukuma ta Onicha a Ebonyi ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta yi Allah wadai da harin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abakaliki, Ebonyi - Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe basarake a jihar Ebonyi, Eze Josephat Ikegwu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba 1 ga watan Afrilun shekarar 2026.

Yan bindiga sun harbe Sarki a gidansa
Taswirar jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabas a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Marigayin shi ne Sarkin al’ummar Ishinkwo da ke karamar hukumar Onicha, kamar yadda rahoton The Nation ya ce.

Kisan Sarki: Yadda al'umma suka dimauce

Kara karanta wannan

Rashin taya Trump yaki da Iran ya harzuƙa shi, ya ci mutuncin Shugaban Faransa da matarsa

An tabbatar da cewa mutuwarsa ta jefa al’umma cikin jimami da firgici mai yawa da fargaba kan hare-hare.

Majiyoyi sun ce harin ya faru da misalin karfe 10:00 na dare, lokacin da maharan suka kutsa gidansa suka harbe shi ta taga yana hutawa.

An ce yana cikin dakinsa tare da matarsa lokacin da aka bude masa wuta ta taga, lamarin da ya janyo mutuwarsa nan take ba tare da jinkiri ba.

Shugabar karamar hukumar Onicha, Ikechukwu Ogbuofia, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa abin bakin ciki ne da ya girgiza yankin sosai.

Ta ce ta samu labarin cewa maharan sun shiga gidansa sannan suka harbe shi ta taga, tana mai nuna alhini kan wannan mummunan aiki.

Yan sanda sun fara binciken kisan basarake a Ebonyi
Sufeta-janar na yan sanda a Najeriya, Ridwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Abin da rundunar yan sanda ta ce

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, Joshua Ukandu, ya kuma tabbatar da aukuwar lamarin tare da cewa an fara bincike, cewar Premium Times.

Ya ce rundunar ‘yan sanda ta samu rahoto kan lamarin, kuma ta kaddamar da bincike domin gano wadanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su.

Kara karanta wannan

Matakai 2 da Tinubu ya dauka da aka kashe Musulmai da Kiristoci a Jos

Wannan kisan ya zo ne kasa da wata guda bayan rasuwar wani Sarki a Ebonyi, Francis Igwe na Ndufu-Alike da ke Ikwo.

An sace shi ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa coci, kuma ya mutu washegari sakamakon raunukan da ya samu a hannun masu garkuwa.

Daga bisani an gano gawarsa bayan mako guda inda aka kai ta dakin ajiye gawa, abin da ya kara firgita jama’ar yankin.

Hukumomin ‘yan sanda sun sanar da cafke mutane tara da ake zargi da hannu a sace shi da kuma mutuwarsa, yayin da bincike ke ci gaba.

Yan bindiga sun harbe dattijuwa matar Sarki

Mun ba ku labarin cewa ’yan bindiga sun kai mummunan hari Kabe a karamar hukumar Borgu, inda suka bindige matar Sarkin Noma yayin da jama’a ke tserewa.

Mazauna sun ce harin ya faru ne da dare, inda aka fasa shaguna, aka sace kayan abinci, inda kauyuka da dama suka fara watsewa.

Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar Neja ke cewa tana daukar matakai domin magance matsalar 'yan bindiga da sauran 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.