Kano: DSS Ta Gano Wurin da Wata Mata ke Samo Makamai Tana Kai wa Ƴan Bindiga a Katsina
- Jami'an hukumar DSS sun kama wata mata mai shekaru 25 da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga harsasai a Kano
- An cafke ta da harsasai 200 da aka ce an kawo daga wata jiha, inda ta shirya safararsu ta Kano zuwa ga ƴan bindiga a Katsina
- Ta amsa laifi tare da fallasa wasu da ake zargin suna da hannu a harkar, har da wanda ya ɗora ta a muguwar sana'ar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta samu nasarar kama wata mata mai suna Nafisa Usman, mai shekaru 25, bisa zargin yana yi wa ƴan ta'adda aiki.
Jami'an sun kama ta da zargin safarar harsasai da ta ke amso wa daga wata jihar domin kai wa ‘yan bindiga da ke addabar jihohi daban-daban a Arewa.

Source: Original
Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an cafke Nafisa ne a waga babban tashar mota da ke Kano, inda aka same ta dauke da sababbin harsasai guda 200.
An kama mai safarar makamai a Kano
Rahotanni sun nuna cewa an kwaso harsasan ne daga Lafiya a jihar Nasarawa, ana kuma shirin kai su Kankara da ke jihar Katsina.
A cewar majiyar, jami’an DSS sun gudanar da wannan aiki bayan samun sahihan bayanan sirri da suka bayyana motsin Nafisa da ayyukanta.

Source: Facebook
Majiyar ta ce:
“Nafisa, ‘yar asalin kauyen Zango a karamar hukumar Kankara, an kama ta ne kafin ta kai kayan ga wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne da ke cikin dajin Kankara.”
Ta kuma kara da cewa matar ta amsa cewa ta shafe watanni biyu tana wannan haramtacciyar sana’a ta safarar makamai da harsasai ga masu aikata laifuffuka.
Yadda Nafisa ke safarar makamai
A yayin bincike, majiyar ta bayyana cewa Nafisa ta ce wani mutum da ake kira “Teso” ne ya ba ta harsasan, inda ta zarge shi da aiki tare da wani jami’in soja da ke zaune a Lafiya, jihar Nasarawa.
Har ila yau, ta amsa cewa ta taimaka wajen gudanar da mu’amaloli da kudinsu ya haura N5m ta tashar mota ta Unguwa Uku a Kano, domin jigilar kayan zuwa Katsina.
Majiyar ta kara da cewa:
"An tsara kai kayan ne ga wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Mallam Haruna, wanda ake zargin yana aiki a yankin Kankara. Ta kuma bayyana cewa tana kai wa wasu da ake kira Buba da Abu harsasai a wannan daji.”
Nafisa ta bayyana cewa wani dillalin dabbobi da ke Kano mai suna Sulaiman ne ya hada ta da ƴan bindiga sannan ya ɗora ta a kan sana'ar.
Wannan samame na DSS na daga cikin matakan da hukumar ke dauka domin rusa hanyoyin samar da makamai ga ‘yan ta’adda, tare da dakile ayyukan ta’addanci da kuma tabbatar da tsaron kasa.
DSS ta ceto jami'in gwamnatin Kano
A baya, kun ji cewa jami’an tsaron farin kaya ta DSS sun ceto sakataren ƙaramar hukuma da wasu 'yan ta'adda suka sace daga gidansa a Kano.
Hukumar ta samu nasarar kama matasa biyu daga cikin wadanda ake zargi yayin da wasu suka tsere da raunukan harbi kuma an shiga nemansu ruwa a jallo.
Masu garkuwar sun shiga gidan jami'in gwamnatin ana bikin Sallah, suka sace shi sannan suka nemi kuɗin fansar Naira miliyan 300 saboda yana gwamnati .
Asali: Legit.ng


