Tinubu Zai Ziyarci Jihohi 4, Zai Fara da Jos inda Aka Kashe Musulmai da Kiristoci

Tinubu Zai Ziyarci Jihohi 4, Zai Fara da Jos inda Aka Kashe Musulmai da Kiristoci

  • Shugaba Bola Tinubu ya dage ziyarar jihar Ogun ta gobe Laraba domin ya ziyarci birnin Jos don jajantawa mutanen da hare-hare suka shafa
  • Bayan ziyarar Plateau, shugaban zai wuce birnin Legas domin gudanar da bukukuwan Good Friday da Easter tare da kaddamar da ayyuka
  • A ranar 4 ga watan Afrilu, shugaban kasar zai kaddamar da filin jirgin sama na Gateway dake jihar Ogun domin bunkasa tattalin arzikin kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya sauya fasalin ziyarar da ya shirya kai wa jihohi huɗu na ƙasar nan tun daga yau Laraba, 1 ga Afrilu, 2026.

Maimakon tafiya garin Iperu dake jihar Ogun gobe kamar yadda aka tsara, shugaban zai garzaya Jos, babban birnin jihar Plateau, domin jajantawa gwamnati da al'umma kan hare-haren 'yan bindiga na baya-bayan nan da suka lakume rayukan bayin Allah.

Kara karanta wannan

Ganduje ya fadi me ya tattauna da Tinubu bayan sauya shekar Kwankwaso, Gawuna

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai ziyarci jihohi 4 a cikin kwanaki 10.
Shugaba Bola Tinubu ya gana da gwamnan Filato, Caleb Mutfwang. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tinubu zai ziyarci Jos, Legas, Ogun

Mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana sabon jadawalin tafiye-tafiyen Tinubu a cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na X.

Bayan kammala ziyarar ta'aziyya a Plateau, Shugaba Tinubu zai wuce birnin Legas domin gudanar da bukukuwan Good Friday.

A ranar Asabar, 4 ga watan Afrilu, shugaban zai koma jihar Ogun domin kaddamar da Filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Gateway International Cargo Airport.

Hakazalika, zai kaddamar da jiragen kasuwanci guda biyu da za su rinka safarar kayayyaki zuwa ƙasashen waje da kuma sabon babban ofishin rundunar kwastam ta tarayya (FOU) da kuma motocin sintiri na zamani.

Tinubu zai kaddamar da ayyuka a Legas

Yayin da yake ci gaba da hutun Easter a Legas, shugaban zai kaddamar da wasu muhimman ayyukan more rayuwa da gwamnatin Gwamna Babajide Sanwo-Olu ta kammala.

Kara karanta wannan

2027: Minista na 3 ya mika wa Tinubu takardar murabus, zai tsaya takarar gwamna

Waɗannan sun haɗa da:

  • Gagarumar gadar nan ta Ojota/Opebi Link Bridge.
  • Katafaren ginin nan na cibiyar bayanan yanayin kasa ta Legas (GIS).
  • Wani katafaren ginin hukumomi da aka sanya wa sunan shugaban ƙasar kansa.
Shugaba Tinubu zai ziyarci jihohi 4 cikin kwanaki 10 inda zai fara da Filato.
Shugaba Bola Tinubu ya na daga wa wadanda suka yi masa rakiya hannu da zai shiga jirgi. Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

Ziyara zuwa jihar Bayelsa

Kafin ya koma fadar shugaban ƙasa dake Abuja, Shugaba Tinubu zai kai ziyara jihar Bayelsa a ranar 10 ga watan Afrilu, kamar yadda sanarwar Onanuga ta nuna.

Shugaba Tinubu zai kai ziyarar ne domin taya Gwamna Duoye Diri kaddamar da wasu daga cikin manyan ayyukan da ya kammala a jiharsa.

Wannan ziyarce ziyarce na kwanaki 10 yana nuna yunƙurin gwamnatin tarayya na ƙarfafa haɗin kai tsakanin jihohi da kuma nuna kulawa ga matsalolin tsaro da na tattalin arziƙi a lokaci guda.

'An kashe Musulmai 4 a Jos' - JNI

A wani labari, mun ruwaito cewa, kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta bayyana adadin Musulman da aka kashe a wani hari da aka kai a Filato.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shirya karbo bashin sama da Naira tiriliyan 8, ya tura sako Majalisar Dattawa

Hakan na zuwa ne bayan wasu 'yan ta'dda sun kai harin mai uwa da wabi kan jama'a da dare a jihar Filato, inda sama da mutum 20 suka mutu.

A yanzu haka dai kungiyar JNI ta sanar da cewa akalla Musulmai 10 ne ba a san a ina suke ba tun bayan harin da aka kai kuma ana neman su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com