Waspapping: Matashin da DSS T Kama a Najeriya kan Yakin Iran Ya Fadi Masu Hannu a Tsare Shi

Waspapping: Matashin da DSS T Kama a Najeriya kan Yakin Iran Ya Fadi Masu Hannu a Tsare Shi

  • Sarki Waspapping, wanda ake zargin jami'an tsaro sun kama shi saboda ya yi magana kan yakin Iran ya shaki iskar 'yanci
  • Fitaccen mai amfani da kafafen sada zumunta ya musanta zargin cewa NSA Nuhu Ribadu ne ya aiko jami'an DDS suka kama shi
  • Matashin ya yi bayanin abin da ya faru tun daga lokacin da aka cafke shi a Kaduna har zuwa taimakon da ya samu aka sake shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Fitaccen mai amfani da kafafen sada zumunta, Sani Buhari, wanda aka fi sani da Sarki Waspapping, ya fito ya yi karin haske game da kama shi da jami’an tsaro suka yi kwanan nan.

Ya musanta jita-jitar da ke cewa Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA) ne ya sa aka kamo shi.

Kara karanta wannan

Trump ya gindaya sharudan tsagaita wuta, ya fadi rokon da Iran ta yi masa

Sarki Waspapping.
Fitaccen mai amfani da kafafen sada zumunta, Sani Buhari (Sarki Waspapping) Hoto: @Waspapping
Source: Twitter

A cikin wani sako da ya fitar shafinsa na X ranar 1 ga watan Afrilu, 2026, Sani Buhari ya bayyana dalla-dalla yadda abubuwan suka faru tun daga ranar da aka kama shi har zuwa lokacin da aka sake shi

Tun farko dai an yada jita-jitar cewa jami'an tsaro sun kama matashin ne kan maganganun da ya yi na nuna goyon baya ga Iran da kuma sukar Amurka da Isra'ila.

Yadda aka kama matashin a Kaduna

A cewar Sani Buhari, jami’an tsaro na farin kaya (DSS) ne suka kama shi a ranar 6 g Maris, 2026, a daidai NEPA Roundabou da ke Kaduna.

Ya bayyana cewa kama shi din ya zo ne ba-zata, kuma a lokacin ba a yi masa wani bayani kan dalilin yin hakan ba. Washegari kuma aka wuce da shi zuwa Abuja bisa umarnin Shugaban Hukumar DSS na Kasa.

Kara karanta wannan

Amurka ta ci karo da cikas, Iran ta illata ta a yakinta da kasar Isra'ila

Batun hannun ofishin NSA

Sarki Waspapping ya jaddada cewa a tsawon lokacin da yake tsare, babu wani lokaci da aka sanar da shi cewa Ofishin NSA ne ya ba da umarnin kama shi.

"Ko sau daya ba a ambaci sunan NSA ba dangane da tsare ni. Hasali ma, gwargwadon bincikena, Ofishin NSA ma bai san halin da nake ciki ba a lokacin da abin ya faru," in ji shi.

Ya bayyana cewa an yi kokari daga bangarori daban-daban domin ganin an sake shi amma abin bai yiwu ba, har sai lokacin da wani abokinsa ya tuntubi wani jami’i a Ofishin NSA.

Yadda Waspapping ya kubuta daga DSS

Wannan jami’in ne ya shiga maganar ta hanyar tuntubar shugabancin DSS, wanda hakan ya kawo sauyi cikin gaggawa ga yadda ake tafiyar da lamarinsa.

Waspapping ya bayyana cewa duk da bai san irin tattaunawar da aka yi a cikin gida ba, amma daga shigar Ofishin NSA cikin maganar, sai tsarin sakin nasa ya sauya kuma ya samu ’yancinsa.

Kara karanta wannan

Yayin da ta ke tsaka da yaki da Iran, Isra'ila ta fadi kasar da za ta mamaye

Dakarun DSS.
Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a bakin aiki Hoto: @DSS_NG
Source: Facebook

Sarki Waspapping ya bayyana cewa ba shi da ma'ana a ce ofishin da ake zargin shi ya sa aka kama mutum, kuma shi ne zai sake tsayawa tsayin daka wajen ganin an sake shi.

Haka kuma, ya jinjina wa hukumar DSS inda ya bayyana su a matsayin kwararru wadanda suka girmama hakkinsa na dan adam a tsawon lokacin da yake tsare a hannunsu.

Amnesty ta yi soki kama Sarki Waspapping

A baya, kun ji cewa Kungiyar Amnesty ta yi Allah-wadai da tsare wani mai tasiri a shafukan sada zumunta a Kaduna kan sakonninsa game da yakin Amurka da Isra’ila da Iran.

Ta ce yanayin da aka kama shi a ciki ya tayar da hankali matuka kan yadda ake gaza girmama dokokin kasa da kuma da kare hakkokin bil’adama a Najeriya.

Kungiyar ta kara da cewa Waspapping shi ne mutum na biyu da aka ruwaito cewa SSS ta tsare dangane maganganun da mutane ke fada kan yakin Iran da Amurka/Isra'ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262