Bayan Dogon Lokaci, Kotu Ta Yi Zama kan Kisan Gillar da Aka Yiwa Fatima da Yaranta 6 a Kano

Bayan Dogon Lokaci, Kotu Ta Yi Zama kan Kisan Gillar da Aka Yiwa Fatima da Yaranta 6 a Kano

  • Babbar kotun jihar Kano ta fara zaman sauraron shari'ar wadanda ake zargi da kisan Fatima da 'ya'yanta shida a unguwar Dorayi a Kano
  • Masu gabatar da kara sun karanto duka tuhume-tuhumen da ake wa wadanda ake zargi su hudu a zaman yau Laraba, 1 ga Afrilu, 2026
  • Babban Lauyan Gwamnati kuma Sakatare Ma'aikatar Shari'a ta Jihar Kano, Salisu Muhammad Tahir ya yi bayanin yadda zaman ya kaya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - An fara sauraron shari'ar mutanen da ake zargi da kisan matar aure, Fatima Abubakar da ya'yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin garin Kano.

Rahotanni sun nuna cewa an gurfanar da wadanda ake zargi su hudu a gaban Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Bompai, a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Kotu ta sake dage shari'ar El-Rufa'i, zai san makomarsa nan da makonni 2

Yaran Fatima.
'Ya'yan Fatima da ake zargin wasu mutane sun kashe su a Dorayi Chiranchi Hoto: Muhammad Ahmad
Source: Facebook

An gurfanar da wadanda ake zargi su 4

Daily Trust ta ce wadanda ake zargi, Umar Auwalu, Yakubu Dayyabu, Isyaka Yakubu, da Umar Alisuna fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi kisan kai, fyade, fashi da makami, da kuma kone-kone.

Yayin zaman kotun, mutane uku daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifuffukan da da aka bayyana, sun ki amsa laifi yayin da wanda ake kara na farko, Umar Auwalu, ya amsa mafi yawancin tuhume-tuhumen.

Sai dai, bisa tanadin doka game da laifuffukan da ka iya kaiwa ga hukuncin kisa, kotun ta rubuta cewa "bai amsa laifin ba" domin ba shi damar kare kansa.

Gwamnatin Kano ta shirya gabatar da shaidu

Jagoran masu gabatar da kara, Saleh Muhammad, ya tabbatar wa kotun cewa gwamnatin Kano a shirye take ta gabatar da hujjoji da kuma kiran shaidu domin tabbatar da zargin da ake yi wa mutanen.

Yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaman, Babban Lauyan Gwamnati kuma Sakatare Ma'aikatar Shari'a ta Jihar Kano, Salisu Muhammad Tahir, ya ce sun shigar da duka tuhume-tuhumen da ya dace da abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Matakin da alkali ya dauka kan bukatar beli a shari'ar El Rufai da hukumar ICPC

Ya ce tuhume-tuhumen suna kunshe ne a cikin kararraki guda uku daban-daban—K-54, K-55, da K-56—wadanda suka shafi abubuwan da suka faru a Tudun Yola, Dorayi Chiranchi, da kuma tuhumar da ta shafi fyade.

Kotu.
Gudumar da ake amfani da ita a kotu da sarkar kama mai laifi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dalilin da ya sa kotu ta dage zama

Ya bayyana cewa yayin da aka karanta tuhume-tuhume a cikin kararraki guda biyu, ba a saurari kara ta uku ba saboda rashin lauyoyin da za su kare wasu daga cikin wadanda ake zargin.

“Ba za ka iya ci gaba da shari’ar kisan kai ba tare da lauya ba, saboda shari’a ce ta rayuwa da mutuwa,” in ji shi.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranakun 22, 27, da kuma 28 ga watan Afrilu, 2026 domin ci gaba da shari’a da kuma gabatar da shaidu, kamar yadda Aminiya ta rahoto.

Gwamna ya yi alkawarin yiwa Fatima adalci

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin nemanwa Fatima da yaranta adalci bisa doka bayan kisan gilla a Dorayi.

Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin mummunan aiki na rashin imani, marar dalili, kuma babban cin mutunci ga darajar ɗan Adam.

Abba ya yi gargaɗi cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada ba tare da rangwame ko da ƙalilan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262