Kotu Ta Sake Dage Shari'ar El Rufa'i, Zai San Makomarsa nan da Makonni 2
- A yau, 1 ga watan Afrilu, 2026 kotu ta sake zama a kan shari'ar da gwamnatin Najeriya ke yi da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i
- Zaman na yau na zuwa ne bayan an dage zaman farko da aka yi bayan rasuwar mahaifyar Malam El-Rufa'i a ranar Litinin
- A zaman shari'ar na yau hukumar ICPC ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda 10 da ake zargin ya karya dokar Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Wata babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta dage sauraron bukatar beli da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai.
Mai shari’a Rilwanu Aikawa ne ya sanya ranar bayan sauraron hujjojin bangaren kare wanda ake tuhuma da kuma masu gabatar da kara a ranar Laraba 1 ga watan Afrilu, 2026.

Source: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta, (ICPC), ce ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotun.
ICPC ta mayar da Nasir El-Rufa'i kotu
Daily Post ta wallafa cewa hukumar ICPC ta kai El-Rufa'i gaban kotun a kan tuhume-tuhume guda 10 da suka shafi zargin karkatar da kadarorin gwamnati da kuma halatta kudin haram.
Sai dai tsohon gwamnan ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa, inda ya ce ba shi da laifi a kan dukkannin tuhume-tuhumen.
Kotun ta bayar da umarnin cewa El-Rufai zai ci gaba da zama a hannun ICPC har zuwa ranar da aka sanya domin sauraron bukatar belinsa.
El-Rufa'i: Yadda zaman kotu ya wakana
Rahotanni sun nuna cewa Nasir Ahmad El-Rufai ya isa harabar kotun da misalin karfe 9:00 na safe a cikin mota kirar Hilux baki, tare da rakiyar jami’an DSS.

Source: Twitter
An gan shi sanye da riga mai launin kasa da hula, a cikin nutsuwa yayin da ya shiga dakin kotu domin fuskantar shari’ar.
Bayan kammala zaman kotun, daya daga cikin lauyoyin da ke kare shi, Ubong Akpan (SAN), ya tabbatar wa manema labarai cewa an dage sauraron karar.
Sai dai ya ce shugaban tawagar lauyoyin ne zai yi karin bayani ga manema labarai daga baya, inda ya tabbatar da dage karar zuwa ranar 14 ga Afrilu, 2026.
Ana sa ran za a ci gaba da sauraron bukatar beli a ranar da kotu ta sanya, yayin da shari’ar ke ci gaba da jan hankalin jama’a.
Dalilin ICPC na sakin El-Rufa'i
A baya, mun wallafa cewa hukumar yaki da cin hanci da sauran laifuffuka masu alaka (ICPC) ta saki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
Majiyoyi daga hukumar sun bayyana dalilin da ya sanya aka saki El-Rufai bayan ya kwashe kwanaki a tsare duk da ba a samu wani umarnin kotu ba.
Sakin El-Rufai dai na zuwa ne bayan mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai, ta yi ban kwana da duniya a birnin Cairo na kasar bayan ta yi rashin lafiya.
Wanda ya tantance Marfeel, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

