Babban Taron APC Ya Ci Rayuka, Hadimin Gwamna da Kansiloli 2 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya

Babban Taron APC Ya Ci Rayuka, Hadimin Gwamna da Kansiloli 2 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Mambobin jam’iyyar APC uku daga jihar Kebbi sun mutu yayin da ake gudanar da babban taron jam'iyya mai mulki na kasa a Abuja
  • Wadanda suka rasu sun hada da kansiloli biyu, Hadiza Sabo Warrah da Sahabi Alheri, sai kuma hadimin gwamnan Kebbi, Abubakar Sadiq
  • Gwamna Nasir Idris ya yi ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da addu’ar Allah gafarta masu, Ya bai wa makusantansu hakuri da juriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon.shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria – A kalla mutane uku sun rasa rayukansu yayin da ake gudanar da babban taron jam’iyyar APC mai mulki, wanda aka kammala a makon jiya a Abuja.

Wadanda suka rasa rayukansu sun hada da kansiloli biyu da wani hadimin gwamna, kuma bayanai sun nuna cewa dukansu daga jihar Kebbi suka fito.

Jami'an FRSC.
Motocin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a bakin aiki Hoto: @FRSCNig
Source: Twitter

Hadimin gwamna da kansiloli 2 sun rasu

Kara karanta wannan

Mamaki ya kama Isra'ila da makaman Iran suka lalata dakunan kariyarta

Jaridar Leadership ta rahoto cewa wadanda suka mutu sun hada da Hadiza Sabo Warrah, kansilar mazabar Warrah da Sahabi Alheri, kansilan mazabar Birnin Yauri, duka a karamar hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi.

Mutum na uku da ya rasa rayuwarsa sanadin taron na APC shi ne Abubakar Sadiq, babban mataimaki na musamman ga Gwamna Nasir Idris a fannin kafofin sada zumunta.

Jam'iyyar APC ta gudanar da babban taronta na kasa ne a ranakun Alhamis da Juma'a, 26 da 27 ga watan Maris, 2026.

Taron ya samu halartar manyan jiga-jigai kamar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima da dubban magoya baya daga lungu da sako na kasar nan.

Yadda hatsarin mota ya rutsa da 'yan APC

A lokacin wannan taro ne, hadimin gwamnan Kebbi da kansiloli biyu da muka ambata a sama suka rasa rayukansu a hatsarin mota da ya rutsa da su kafin su karisa wurin taron a Abuja.

A cewar sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kebbi, Yahaya Sarki, ya fitar, wadannan mutane uku sun mutu ne bayan wata mota ta kade su a bakin hanya.

Kara karanta wannan

Rundunar IRGC ta yi wa Isra'ila barna a sababbin hare haren makami mai linzami

Ya ce motar ta kade su ne yayin da suke kokarin tsallaka titi bayan motarsu ta tsaya a hanya a lokacin da suke kan hanya don halartar taron APC, cewar rahoton Daily Post.

Gwamna Nasir.
Gwamnan jihar Kebi, Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu) Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Gwamnan Kebbi ya yi ta'aziyya

Gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, a cikin sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, ya bayyana cewa labarin mutuwarsu ya girgiza shi kuma ya roki Allah ya gafarta musu zunubansu.

Nasir Idris ya kara da cewa mutanen da suka mutu sun bar gibi a harkokin ci gaban jihar Kebbi, inda ya yi addu'ar Allah Ya bai wa iyalansu hakurin jure wannan rashi.

Wakilan APC 3 sun mutu a hatsarin mota

A wani rahoton, kun ji cewa akalla wakilan jam’iyyar APC uku daga karamar hukumar Ogbadibo a Benue sun rasu a hatsarin mota da ya rutsa da su a Nasarawa.

Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne yayin da suke hanyar zuwa Lafia, babban birnin jihar Nasarawa inda wasu 10 suka jikkata sakamakon hatsarin mota mai muni da ya afku.

Wani babban jami’in APC ya bayyana cewa motar bas da ke dauke da wakilan ta kwace, ta fada cikin daji, inda uku suka mutu, sauran kuma suka samu raunuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262