Tarihin Dan Amurka da ke Yawo a Arewacin Najeriya Yana Cewa a Dauki Makami
- Hankulan 'yan Najeriya sun fara karkata kan wani matashi dan kasar Amurka da ya ke yawo a jihohin Arewa ta Tsakiya a kwanan nan
- Matashin mai suna Alex Barbir ya fara yawo a kauyukan Najeriya ne bayan da maganar zargin kisan Kiristoci ta yadu a fadin duniya
- Rahotanni sun nuna cewa an haifi Barbir ne a Agustan 1997 a kasar Amurka, inda a yanzu ya ke kira ga mutane su dauki makami a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bayan bayyanar wani matashi ɗan Amurka mai suna Alex Barbir, mutane da dama a ƙasar sun fara tambaya kan tarihinsa da inda ya fito.
Ya fito a wani bidiyo yana sukar shugaban Najeriya, Bola Tinubu bayan wani hari da 'yan ta'adda suka kai suka kashe Musulmi da Kirista a Filato.

Source: Twitter
BBC Hausa ta wallafa cewa Alex ya yi kira ga mutanen da hare-hare suka shafa da su ɗauki matakan kare kansu, har ma ya ƙarfafa su.
Waye dan Amurka, Alex Barbir?
Barbir yana cikin waɗanda ke nuna damuwa kan abin da ya kira kisan gilla ga Kiristocin Najeriya, ikirarin da wasu ƴan Najeriya, ciki har da wasu Kiristoci, suka musanta.
Game da asalinsa, bayanan da aka tattara sun nuna cewa Alex Barbir ɗan ƙasar Amurka ne mai gudanar da ayyukan jinƙai a Najeriya.
An bayyana cewa cikakken sunansa Alex Daniel Barbir, an haife shi ne a ranar 17 ga watan Agusta, 1997, a Lawrenceville da ke jihar Georgia a Amurka.

Source: Twitter
A baya, ya shahara a harkar wasanni musamman guje-guje da tsalle-tsalle da kuma wasan ƙwallon ƙafa. Sai dai a shekarar 2018 ya dakatar da ƙwallo ya koma karatu a Jami’ar Liberty a fannin likitanci.
Rahotanni sun nuna cewa daga baya ya koma aikin jinƙai ƙarƙashin wata ƙungiya da ke tallafa wa waɗanda suka fuskanci wahalar rayuwa.
Maganar kira a dauki makami
A wani bayani da ya yi, rahotanni sun nuna cewa ya yi magana game da Fulani makiyaya, yana kira ga jama'a su dauki makami do kare kai.
Ya ce:
"Maharan Fulani ne kuma suna yin abin da suke yi ne a matsayin Jihadi...Kuma gwamnati ta na taimaka musu...saboda haka ya kamata ku tashi ku kare kanku...ina bindigoginku?"
A wani bidiyon da ya wallafa a shafinsa na X, Alex ya ce:
"Yanzun nan suka kashe mutum 10. Kiristoci da ba su ji ba, ba su gani ba a ranar Lahadi. Tinubu, ka na ina a lokacin da ake kashe mutanenka cikin dare?"
Ga bidiyon bayanin da ya yi a kasa:
An nemi a kama Alex Babir
A wani labarin, mun kawo muku cewa 'yan Najeriya sun fara magana kan dan kasar Amurka da aka gani yana yawo a jihohin Arewa ta Tsakiya.
Wasu masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun bukaci gwamnatin Najeriya ta bincike shi domin tabbatar da hakikanin aikin da ya zo yi.
Duk da kiran da ake yi, wasu masana sun nuna shakku kan cewa za a iya binciken shi lura da cewa daga kasar Amurka ya fito.
Asali: Legit.ng

