Lamari Ya Girma: Sanatan Amurka Ya Bankado ‘Sirrin’ Wasu Manyan Najeriya

Lamari Ya Girma: Sanatan Amurka Ya Bankado ‘Sirrin’ Wasu Manyan Najeriya

  • Dan majalisa a Amurka, Ted Cruz ya zargi wasu jami’an gwamnatin Najeriya da taimaka wa cin zarafin Kiristoci
  • Harin unguwar Rukuba da ke birnin Jos ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 30 a ranar 'Palm Sunday' a karshen mako
  • Caleb Mutfwang ya yi alkawarin hukunta masu laifi, yayin da aka sanya dokar kulle na sa’o’i 48 a Jos ta Arewa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Sanatan Amurka, Ted Cruz, ya yi magana mai zafi kan harin da aka kai al'umma da ke Jos a jihar Plateau.

Crus ya yi zargin cewa gwamnatin Amurka ta gano wasu jami’an Najeriya da ke haifar da yanayin da ke bai wa damar cin zarafin Kiristoci a kasar, tare da cewa suna da hanyoyin ladabtar da su.

Kara karanta wannan

Yayin da ta ke tsaka da yaki da Iran, Isra'ila ta fadi kasar da za ta mamaye

Sanatan Amurka ya zargi manyan Najeriya a kisan Kiristoci
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Donald J Trump.
Source: Twitter

Harin Plateau ya girgiza sanatan Amurka

Hakan na cikin wata sanarwa da rubutu da Cruz ya fitar wanda jaridar Punch ta samu a yau Talata 31 ga watan Maris din shekarar 2026.

Ya yi hakan ne domin martani kan harin da aka kai a unguwar Rukuba da ke karamar hukumar Jos ta Arewa, wanda ya faru a ranar 'Palm Sunday' kuma ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 30.

Ya ce:

“Wasu jami’an gwamnatin Najeriya sun kirkiro yanayi da ke sa ake yawan cin zarafin Kiristoci tare da kashe su, ta hanyar aiwatar da dokar Shari’a da kuma yin watsi da tashin hankali.
“Ya kamata wadannan jami’ai su sani cewa Amurka ta san su, kuma tana da kayan aikin da za ta hukunta su.”

Rundunar ‘yan sandan jihar Plateau ta ce ‘yan bindiga sun kai harin unguwar Rukuba da misalin karfe 8:30 na dare a ranar 29 ga Maris, inda suka kashe mutane 30 sannan an gano karin gawarwaki biyu daga daji yayin bincike.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Jos ya dauki hankalin Amurka, dan majalisa ya shawarci Tinubu

Harin ya jawo martani daga wani Ba’amurke, Alex Barbir, wanda ya soki Bola Ahmed Tinubu kan abin da ya kira gazawar gwamnati wajen daukar mataki.

Ya ce:

“Sun kashe fiye da mutane 10, Kiristoci marasa laifi a ranar Palm Sunday. Tinubu, ina kake yayin da ake kashe jama’arka da dare?”
Gwamna ya jajantawa wadanda harin Jos ya shafa
Gwamna Caleb Mutftwang na jihar Plateau. Hoto: Caleb Muftwang.
Source: Facebook

Martanin Gwamna Caleb kan hari

A bangarensa, gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya ziyarci yankin tare da jaddada cewa za a hukunta masu aikata laifin, cewar The Sun.

Ya ce:

“Radadin da ku ke ji, shi mu ke ji muma baki daya, gwamnati za ta tabbatar an gurfanar da masu laifi a gaban kuliya.”

Gwamnan ya kuma sanar da cewa gwamnati za ta biya kudin jinyar wadanda suka jikkata tare da shirya jana’izar da ta dace ga wadanda suka rasu.

Bayan harin, an sanya dokar hana fita ta sa’o’i 48 a karamar hukumar Jos ta Arewa daga tsakar dare na ranar 29 ga Maris zuwa 1 ga Afrilun 2026.

Kisan Jos: Dan majalisar Amurka ya shawarci Tinubu

A baya, an ji cewa dan majalisa daga Amurka, Riley Moore ya yi magana kan harin da aka kai a Jos a ranar Lahadi 29 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta illata Isra'ila, ta babbake wani babban kamfani a farmakin da ta kai

Moore ya soki hare-haren da aka kai wa Kiristoci a Jos, ya bukaci Najeriya ta ƙarfafa tsaro domin kare lafiyar al'ummar kasar.

Ya gargadi cewa ci gaba da kashe-kashe na iya lalata dangantakar diflomasiyya tsakanin Amurka da Nigeria.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.