Diflomasiyya: Jerin kasashe 10 da suka amince da naɗin sabbin jakadun Najeriya

Diflomasiyya: Jerin kasashe 10 da suka amince da naɗin sabbin jakadun Najeriya

  • Ma'aikatar harkokin waje ta ce ƙasashe 10 sun aiko da takardun amincewa da sababbin jakadun Najeriya da aka tura musu
  • Daga cikin jakadun da aka amince da su har da tsohon shugaban INEC Mahmud Yakubu da kuma tsofaffin shugabannin hukumomin tsaro
  • Har yanzu ana jiran martani daga Jamus da Mexico kan naɗin Femi Fani-Kayode da Reno Omokri a matsayin jakadun Najeriya a can

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta sanar da cewa ta karɓi takardu daga ƙasashe guda 10 da suka amince da naɗin sababbin jakadun da Shugaba Bola Tinubu ya tura masu.

Kakakin ma'aikatar, Kimibie Ebienfa, ya bayyana cewa ƙasashen da suka amince a nade-naden sun haɗa da Birtaniya, Faransa, Amurka, Ireland, Qatar, Jamhuriyar Benin, Habasha, Djibouti, Senegal da Saliyo.

Kara karanta wannan

Mojtaba Khamenei: Daga karshe an bayyana kasar da sabon jagoran addini na Iran yake

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta lissafa kasashe 10 da suka amince da sababbin jakadun da aka tura masu.
Karamar ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu da ministan waje, Yusuf Tuggar (wanda ya yi murabus). Hoto: @NigeriaMFA
Source: Twitter

Kasashe 10 sun amince da jakadun Najeriya

Jaridar The Cable ta ruwaito Ebienfa, a cikin sanarwar da ya fitar, ya bayyana cewa:

"Ina son sanar da ku cewa har yanzu muna ci gaba da karɓar saƙonnin amincewa daga ƙasashen da aka tura jakadunmu zuwa gare su."

Daga cikin sunayen da ƙasashen suka amince da su, akwai tsofaffin shugabannin hukumomin tsaro da kuma ƙwararrun ma'aikatan diflomasiyya waɗanda aka ba wa muƙaman.

Aminu Dalhatu ne zai wakilci Najeriya a Birtaniya, yayin da tsohon shugaban DSS, Kayode Are, zai ƙasar Amurka. Shi kuwa tsohon shugaban hukumar NIA, Ayodele Oke zai yi aiki a ƙasar Faransa.

Haka kuma, an tabbatar da karbar tsohon shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, a matsayin jakadan Najeriya a ƙasar Qatar.

Jiran martani kan Fani-Kayode da Omokri

Duk da samun amincewar waɗannan jakadu 10, sanarwar ta nuna cewa har yanzu ana jiran martani daga ƙasar Jamus inda aka tura Femi Fani-Kayode, da kuma ƙasar Mexico inda aka tura Reno Omokri.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda yakin Iran da Amurka ya shafi tattalin arziki da tsaron Najeriya

Ma'aikatar ta bayyana cewa:

"Ana sa ran samun saƙon amincewa ga Femi Fani-Kayode da aka tura Jamus, da kuma Reno Omokri wanda aka tura ƙasar Mexico nan ba da daɗewa ba."

Masana diflomasiyya sun bayyana cewa wannan tsari na jiran amincewar ƙasashe abu ne na yau da kullum dake ɗaukar lokaci kafin kowace ƙasa ta tantance wanda aka tura mata, in ji rahoton Punch.

Har yanzu daia ana jiran wasu kasashe da ba su riga sun amince da jakadun da Najeriya ta tura masu ba
Okezie Ikpeazu, Femi Fani-Kayode, da Reno Omokri, da suka shiga jerin sababbin jakadun Najeriya. Hoto: @realFFK, @IkpeazuOkezie, @renoomokri
Source: Twitter

Shirye-shiryen rantsar da da jakadun

Shugaba Tinubu ya riga ya amince da tura ƙwararrun jakadu 31 da kuma wadanda ba ƙwararru ba 34 zuwa ƙasashe daban-daban da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ma'aikatar ta tabbatar da cewa za a sanar da ranar gudanar da taron rantsar da sababbin jakadun da kuma ba su horo da zarar fadar shugaban ƙasa ta kammala shirye-shiryenta.

Tun a watan Satumban 2023 ne shugaban ƙasar ya dawo da dukkan jakadun Najeriya dake ƙasashen waje gida, inda ya fara naɗa sababbi tun a watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Tinubu ya cika shekaru 74 a duniya, ya aika muhimmin sako ga 'yan Najeriya

Kasashe sun ki karbar jakadun Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, Indiya da wasu kasashe sun ki amincewa da wasu daga cikin jakadun da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada kwanan nan.

Wasu manyan jami’ai a fadar shugaban kasa da kuma ma’aikatar harkokin waje sun bayyana cewa Indiya, tana da wata doka da ta dade tana bi wadda ke hana karbar jakadu.

Wasu majiyoyi sun ce gwamnatin tarayya ta riga ta fara samun sakonni daga New Delhi da ma wasu manyan kasashe cewa ba su da niyyar karbar jakadu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com