Tinubu Ya Shirya Karbo Bashin Sama da Naira Tiriliyan 8, Ya Tura Sako Majalisar Dattawa

Tinubu Ya Shirya Karbo Bashin Sama da Naira Tiriliyan 8, Ya Tura Sako Majalisar Dattawa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara bin matakan sake karbo wa Najeriya bashin kudin da suka haura Naira tiriliyan 8
  • A wasu wasiku biyu da ya tura Majalisar dattawa, Tinubu ya ce za a yi amfani da kudin wajen gina ababen more rayuwa da biyan wasu tsofaffin basussuka
  • Majalisar dattawa ta mika bukatun Tinubu ga kwamitin kula da harkokin basussuka na gida da na waje domin yin nazari kuma ya dawo da rahoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika wasiku biyu zuwa Majalisar Dattawa domin neman amincewarta wajen karbo sababbin basussuka daga kasashen waje.

Basussukan da Tinubu ya bukaci Majalisar ta amince ya ciyo wa Najeriya sun kai Dala biliyan 6, kwatankwacin Naira tiriliyan 8.3 a kudin kasar nan.

Kara karanta wannan

Bayan watsi da taron Abba, Sanata Kawu Sumaila ya sa labule da manyan APC

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana aiki a ofishinsa a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Dalilin Tinubu na karbo bashin $5bn

A rahoton Daily Trust, Shugaba Tinubu ya ce zai karbo wannan rance ne domin gudanar da ayyukan more rayuwa, biyan basussuka da kuma gyaran tashoshin jiragen ruwa.

A wasika ta farko da ya aikewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wacce ya karanta a zaman majalisa na ranar Talata, shugaban ya bukaci sanatoci su yi “gaggawar amincewa” da bukatar.

A cikin wannan takardar, Shugaba Tinubu ya nemi amincewar Majalisar domin karbo bashin Dala biliyan 5 daga bankin First Abu Dhabi Bank.

Ya bayyana cewa idan aka amince da wannan bashi, jimillar bashin da ake bin Najeriya zai tashi daga Dala biliyan 110.3 zuwa Dala biliyan 115.3.

Bashin gyaran tashoshin ruwa a Legas

A wata wasika ta daban, Tinubu ya kuma nemi amincewar majalisar dattawa don dauko karin bashin Dala biliyan 1 na gyaran tashar ruwa ta Lagos Port Complex da tashar Tin Can Island Port.

Kara karanta wannan

Domin biyayya ga umarnin Tinubu, minista ya yi murabus daga mukaminsa a Najeriya

Ya ce wannan bashi, wanda Citibank London ya shirya tare da goyon bayan UK Export Finance, zai taimaka wajen sabunta tashoshin jiragen ruwa, Inganta tsaro da aiki don kiyaye ka’idojin kasa da kasa.

Majalisa.
Sanatoci yayin da suke zama a zauren Majalisar dattawan Najeriya Hoto: Senate Nigeria
Source: Facebook

A cewar shugaba Tinubu, bashin zai dauki tsawon shekaru 14 kafin a biya shi, ciki har da shekaru 4 na farko na jinkirin fara biya.

Haka kuma Tinubu ya bayyana cewa akwai kudin samar da bashi na kashi 1.1 da kudin inshora kashi 1.07 cikin 100.

Mataki na gaba da Majalisa ta dauka

Majalisar Dattawa ta mika wasikun bukatun ciyo bashin zuwa kwamitinta mai kula da harkokin basussuka na cikin gida da na waje domin yin nazari.

An umarci kwamitin da ya gaggauta duba bukatun tare da gabatar da rahoto domin yanke hukunci, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

An nemi Tinubu ya tsige shugaban CAC

A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tsige shugaban hukumar CAC, Hussaini Ishaq Magaji.

Rahotanni sun nuna cewa majalisar ta gayyaci shugaban CAC na kasa sau da dama domin ya bayyana a gabanta, amma har yanzu bai amsa ko daya daga ciki ba.

Bisa haka ne Majalisar Dattawan ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya tsige Shugaban Hukumar CAC a matsayin matakin ladabtarwa saboda nuna raini ga Majalisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262