El Rufai Zai Ci Gaba da Zama a hannun ICPC duk da Rasuwar Mahaifiyarsa

El Rufai Zai Ci Gaba da Zama a hannun ICPC duk da Rasuwar Mahaifiyarsa

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai na ci gaba da jimamin rasuwar mahaifiyarsa wadda ta riga mu gidan gaskiya a makon jiya
  • Ana cikin zaman makokin Hajiya Umma El-Rufai, tsohon gwamnan ya bayyana a gaban kotu domin ci gaba da shari'a kan tuhume-tuhumen da ICPC ke yi masa
  • Hakazalika, El-Rufai zai ci gaba da zama a tsare a hannun hukumar ICPC har zuwa lokacin da kotu za ta yi hukunci kan bukatar neman belin da ya gabatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, zai ci gaba da zama a hannun hukumar ICPC.

An mayar da Malam Nasir El-Rufai, hannun hukumar yaƙi da cin hanci da sauran laifuffuka masu alaƙa da hakan (ICPC).

El-Rufai ya koma hannun hukumar ICPC
El-Rufai lokacin da aka raka shi zuwa kotu Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa an mayar da El-Rufai hannun hukumar ICPC ne a ranar Talata, 31 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Matakin da alkali ya dauka kan bukatar beli a shari'ar El Rufai da hukumar ICPC

Naisr El-Rufai ya sake bayyana gaban kotu

Tsohon gwamnan, wanda ya bar hannun ICPC a ranar 27 ga Maris, 2026, biyo bayan rasuwar mahaifiyarsa, an sake gurfanar da shi a farkon ranar Talata.

Kafin nan, kotun ta ɗage saurarar buƙatarsa ta neman belin zuwa ranar 31 ga Maris, 2026.

Amma, a ranar Talata, ya fara bayyana ne a babbar kotun jihar Kaduna kan wata tuhuma ta daban da hukumar ICPC ta shigar kansa.

Rashin halartar wanda ake ƙara na biyu ya dakatar da saurarar ƙarar, inda aka ɗage ta zuwa ranar 10 ga Afrilu, 2026.

Bayan haka, aka tafi da shi zuwa babbar Kotun rarayya da ke Kaduna, wadda aka tsara za ta saurari buƙatarsa ta neman beli.

Jami'an ICPC sun yi wa El-Rufai rakiya

Jim kaɗan bayan tashi daga zaman kotun, jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da sauran laifuffuka masu alaƙa (ICPC) sun raka El-Rufai fita daga harabar kotun a cikin wata farar mota ƙirar Hilux.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya gurfana a kotu ana jimamin rasuwar mahaifiyarsa

Kafin nan, tsohon gwamnan ya koma kotun ne a cikin tsauraran matakan tsaro domin ci gaba da sauraren buƙatarsa ta neman beli.

Bayan kammala zama a babbar kotun jiha, hukumar ta mayar da El-Rufai zuwa babbar kotun Tarayya da ke cikin haraba guda domin ci gaba da sauraron shari’ar.

El-Rufai ya koma hannun hukumar ICPC
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

El-Rufai ya koma hannun ICPC

Sakamakon ɗage zaman da aka yi, ana sa ran a Laraba za a ci gaba da sauraron buƙatar tasa ta neman beli.

Bayan bayyanar tasa a kotu, an mayar da shi hannun hukumar ICPC yayin da ake ci gaba da gudanar da shari’o’in da ake yi kansa, rahoton Vanguard ya tabbatar da hakan.

El-Rufai ya sauke Kur'ani a hannun ICPC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya yi amfani da lokacin da aka tsare shi a hannun ICPC ta hanya mai kyau.

Wani makusancin El-Rufai ya bayyana cewa tsohon gwamnan bai yi asarar lokaci ba, domin ya yi amfani da lokacin da ya kwashe a tsare wajen ibada da karatu mai zurfi.

Ya kara da cewa El-Rufai ya kammala karatun Alƙur’ani mai tsarki gaba ɗaya, ya karanta littattafai guda 10, sannan ya rubuta wasu littattafai a lokacin da yake tsare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng