Yau ce Ranar Karshe: Abin da Ya Kamata Ku Sani kan Cika Bayanan Haraji a Najeriya

Yau ce Ranar Karshe: Abin da Ya Kamata Ku Sani kan Cika Bayanan Haraji a Najeriya

  • A yau Talata, 31 ga watan Maris, gwamnatin tarayya za ta rufe shafin cike bayanan harin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar a bana
  • Gwamnatin tarayya ta bukaci kowane dan kasa da ke aiki ya tura bayanan shi domin tantance nawa zai rika biyan kudin haraji duk shekara
  • Duk wanda bai cika bayanan shi kamar yadda gwamnati ta bukata ba, akwai hukunci na musamman da aka tanada za a masa bisa dokar kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yayin da wa’adin 31 ga Maris, 2026 zai ƙare a yau, bincike ya nuna cewa yawancin masu biyan haraji a Najeriya ba su da cikakken ilimi kan yadda ake shigar da bayanan harajin kudin shiga karkashin sababbin dokokin haraji.

Kara karanta wannan

Amurka ta fara maganar laftawa Larabawa kudin diyya kan yakin Trump da Iran

A ƙarƙashin dokar haraji ta Najeriya, duk wani ɗan Najeriya da ke samun kuɗin shiga wajibi ne ya gabatar da bayanan haraji na shekara-shekara, wanda ke nuna duk abin da ya samu a shekarar da ta gabata.

Taiwo Oyedele da shugaba Bola Tinubu
Wanda ya jagoranci tsara dokokin haraji da Bola Tinubu. Hoto: Taiwo Oyedele
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa ana kula da harajin kudin shiga (PIT) ne ta hukumar haraji ta jiha inda mai biyan haraji yake zaune, ba wai inda ya fito ba. Ga ma’aikata, ana cire haraji kai tsaye daga albashi ta tsarin PAYE.

Haraji: Takardun da ake buƙata

Kafin shigar da bayanan haraji, dole ne mai biyan haraji ya mallaki Lambar Shaidar Haraji (TIN), wacce ke zama wata lamba ta musamman da ake amfani da ita wajen duk harkokin haraji.

Ana iya samun TIN ta yanar gizo ta amfani da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN), ko kuma ta Hukumar Haraji ta Ƙasa ko ta jiha, haka kuma, ana buƙatar takardun albashi ko bayanin kuɗin shiga.

Sauran abubuwan da ake buƙata sun haɗa da bayanan banki, bayanan kuɗin kasuwanci ko aikin hannu, hujjojin cire kuɗi (kamar fansho da inshora), shaidar biyan haya (ga masu neman rangwamen haya).

Yadda tsarin cike bayanan haraji ya ke

Kara karanta wannan

Mayakan Houthi sun shigawa Iran yaki, sun yi ruwan wuta a Isra'ila

Ga ma’aikatan kamfanoni, dole ne su bayyana duk hanyoyin kuɗin shiga da suka samu a shekara, ciki har da albashi, kuɗin kasuwanci ko sana’a, da kuma aikin wucin gadi da sauransu.

Haka kuma, dole ne su haɗa da ribar da suka samu a kasuwanci, kuɗin ruwa, da kuɗin da aka samu daga ƙasashen waje idan akwai.

Taiwo Oyedele a majalisar dattawa
Taiwo Oyedele na bayani kan dokokin haraji a majalisar dattawa. Hoto: Taiwo Oyedele
Source: Facebook

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa ana iya shigar da bayanan ta yanar gizo ta shafin hukumar haraji ta jiha ko kuma a ofisoshin haraji.

Wa ya kamata ya shigar da bayanan?

Ga ma’aikatan da ke ƙarƙashin tsarin PAYE, ana buƙatar su shigar da bayanai idan suna da ƙarin kuɗin shiga idan suna kasuwanci ko suna da hanyoyi da dama na samun kuɗi, ko sun sauya aiki a cikin shekarar.

Bayan shigar da bayanai, za a ba su tabbaci daga hukumar haraji ta jiha, hukumomi za su iya amincewa da bayanan ko su sake tantance su bayan dubawa.

Dole ne shigar da bayanan haraji?

Shigar da bayanan haraji ya zama wajibi a doka ga duk masu samun kuɗin shiga a Najeriya kamar yadda gwamnati ta sha fadin hakan.

Kara karanta wannan

Komai ya fito: Yadda Boko Haram ta saki bama bamai kan masu azumi a Borno

Baya ga guje wa tara, ana buƙatar cike bayanan don samun wasu muhimman ayyuka kamar kwangilolin gwamnati, rance, da neman biza, waɗanda ke buƙatar Takardar Shaidar Biyan Haraji.

Hukuncin wanda ya saba dokar

Sababbin dokokin harajin Bola Tinubu sun bayyana cewa wa’adin shigar da bayanan harajin shi ne 31 ga Maris na kowace shekara.

Saboda haka, wanda ya kasa shigar da bayanai zai iya fuskantar tarar N100,000 a watan farko, sannan N50,000 a kowane ƙarin wata da ya ƙara wucewa.

Haka kuma, doka ta tanadi cewa ƙin biyan haraji da aka tabbatar na iya jawo amfani da ikon gwamnati da ke bai wa hukumomin haraji damar karɓar kudin.

NLC ta yi korafi game da ma'aikata

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar kwadago ta shigar da korafi wajen gwamnatin tarayya kan halin da ma'akata ke ciki a kasar nan.

Kungiyar NLC ta ce kayan masarufi sun tashi a Najeriya, lamarin da ya sanya karin albashin da aka yi a 2025 ba zai yi wani tasiri ba.

A karkashin haka, 'yan kwadago suka bukaci gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta gaggauta fara shirin kara albashin ma'aikata zuwa akalla N150,000.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng