Ministoci na Yin Murabus, Tinubu Ya Yi Muhimman Nade Nade a Gwamnatinsa

Ministoci na Yin Murabus, Tinubu Ya Yi Muhimman Nade Nade a Gwamnatinsa

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sababbin nade-nade a gwamnatinsa, inda ya zakulo mutane daga jihohi daban-daban
  • Mai girma Bola Tinubu ya dauko tsohon sanata daga jihar Katsina ya ba shi mukamin shugaban hukumar yi wa kamfanoni rajista (CAC)
  • Hakazalika Shugaba Tinubu ya nada kwamishinoni bakwai a hukumar kididdigar jama'a ta kasa watau NPC

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar yi wa kamfanoni rajista (CAC).

Shugaba Bola Tinubu ya nada Sanata Ibrahim Ida a matsayin sabon shugaban hukumar CAC.

Tinubu ya yi nade-nade a gwamnati
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 30 ga watan Maris 2026.

A cewar Onanuga, Shugaba Tinubu ya kuma zaɓi mutane bakwai don cike gurabun kwamishinoni da suka rage a hukumar kididdigar jama'a ta kasa (NPC).

Kara karanta wannan

Domin biyayya ga umarnin Tinubu, minista ya yi murabus daga mukaminsa a Najeriya

Wanene sabon shugaban CAC?

Ibrahim Ida yana da digiri na biyu (MSc) a fannin banki da kuɗi daga jami'ar Ibadan (1983) da kuma digirin lauya (LLB) daga jami'ar Abuja (2003).

Kafin zaɓensa a majalisar dattawa a 2017 don wakiltar Katsina ta Tsakiya, ya yi aiki a matsayin kwamishinan kuɗi na jihar Katsina kuma babban sakatare a hukumar kula da ma'aikatan gwamnatin tarayya.

Tinubu ya nada kwamishinoni a NPC

A halin da ake ciki, mutane bakwai da aka zaɓa a matsayin Kwamishinonin Tarayya don wakiltar jihohinsu a Hukumar Ƙididdigar Jama'a ta Ƙasa su ne:

  • Kolawole Oladipupo Alabi (Ekiti)
  • Nasiru Mu’azu (Zamfara)
  • Usman Abubakar Tuggar (Bauchi)
  • Dr. Isaka Alada Yahaya (Kwara)
  • Farfesa Sadiq Isah Radda (Katsina)
  • Suleiman Umar (Jigawa)
  • Hon. Chiso Abdullahi Dattijo (Sokoto)

Waɗannan naɗe-naɗe suna jiran tantancewar majalisar dokoki ta kasa domin amincewa da su.

Tinubu ya yi nade-nade

Shugaban ya kuma naɗa Dr. Yusuf Mohammed daga jihar Kano a matsayin shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Kaltungo a jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci sun yi wa Tinubu saukar Kur'ani sama da sau 100

Tinubu ya nada shugaban hukumar CAC
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Haka zalika, Shugaba Tinubu ya tabbatar da naɗin Bala Mohammed Bello a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan tattalin arzikin siyasa.

Bala Mohammed Bello, wanda ɗan jihar Taraba ne, yana da digirin farko a fannin akanta da kuma digiri na biyu (MBA) daga jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Kafin wannan naɗin, ya kasance mataimakin shugaban babban bankin Najeriya (CBN).

Ya kuma yi aiki a matsayin babban darakta a bankin kula da shigowa da fitar da kayayyaki na Najeriya (NEXIM) daga 2017 zuwa 2022.

Ministan Tinubu ya yi murabus

A wani labarin kuma, kun ji cewa daya daga cikin Ministocin da ke aiki a gwamnatin, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi murabus.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Litinin, 30 ga watan Maris, 2026.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Ambassada Yusuf Tuggar ya ajiye aiki ne domin ya shiga takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi a babban zaɓe na 2027 da ake tunkara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng