'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Zamfara bayan Kai Harin Ta'addanci
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani kazamin harin ta'addanci a jihar Zamfara ta tarayyar Najeriya
- Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a harin da suka kai a karamar hukumar Zamfara
- Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta bayyana irin barnar da 'yan bindigan suka yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - ’Yan bindiga sun farmaki ƙauyen Dangoro da ke gundumar Nahuce, a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutanen ƙauyen waɗanda ba a tantance adadinsu ba, sannan suka ƙona gidaje da rumbunan abinci.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce mazauna yankin sun ce maharan sun shiga kauuen ne a daren ranar Asabar, 28 ga watan Maris 2026.
'Yan bindiga sun yi barna a Zamfara
'Yan bindigan sun riƙa harbe-harbe ba kakkautawa tare da yin barna yayin harin da suka kai.
Mazauna yankin sun yi zargin cewa wata mace mai juna biyu na wata tara tana cikin waɗanda abin ya shafa, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.
Har yanzu ba a tabbatar da ainihin adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba, kodayake waɗanda abin ya shafa sun ce akasarin waɗanda aka tafi da su mata ne.
An kuma ce maharan sun cinna wa gidaje da dama da rumbunan hatsi wuta, lamarin da ya tilasta wa mazauna Dangoro da dama tserewa don neman tsira a garin Nahuce da ke maƙwabtaka da su.
'Yan sanda sun tabbatar da lamarin
Rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da harin a cikin wata sanarwa da Legit Hausa ta samu daga kakakinta, DSP Yazid Abubakar.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 28 ga Maris, 2026, da misalin ƙarfe 10:30 na dare, lokacin da ’yan bindiga ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 suka farmaki ƙauyen Dangoro na gundumar Nahuce, inda suka riƙa harbe-harbe tare da ƙona gidaje da rumbuna.
“Bayan samun rahoton, wata haɗaɗɗiyar tawaga ta jami’an ’yan sanda da mambobin sa-kai sun tashi cikin sauri zuwa wurin."
"Tawagar ta yi musayar wuta da miyagun, inda suka yi nasarar fatattakar su, lamarin da ya tilasta wa masu laifin tserewa zuwa daji tare da yiwuwar samun raunukan harbin bindiga."
- DSP Abubakar Yazid
'Yan sanda sun tabbatar da kashe mutane
Ya ƙara da cewa an kashe mutane uku yayin harin, ciki har da wani mamba na rundunar Askarawan Zamfara yayin da mutane biyar suka samu raunukan harbin bindiga, wasu huɗu kuma suka samu raunukan ƙonewa daban-daban.

Source: Original
“An kwashe dukkan waɗanda suka ji rauni zuwa babban asibitin tarayya (FMC) da ke Gusau, inda a halin yanzu suke karɓar magani kuma suna samun sauki."
- DSP Abubakar Yazid
DSP Abubakar Yazid ya ƙara da cewa maharan sun kuma ƙona gidaje da dama, rumbunan da ke ɗauke da hatsi, da kuma dabbobi da suka haɗa da awaki.
'Yan bindiga sun farmaki taron bikin aure
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai harin ta'addanci a jihar Kaduna.
'Yan bindigan sun farmaki wani taron bikin aure a ƙauyen Kahir da ke karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna.
Tsagerun 'yan bindigan sun kashe mutane 13 tare da yin garkuwa da wasu mutane waɗanda ba a tantance adadinsu ba a yayin harin.
Asali: Legit.ng


