'Yan Bindiga Sun Farmaki Wurin Taron Bikin Aure, an Yi Ta'asa Mai Girma
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Kaduna da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Tsagerun 'yan bindigan sun kashe mutane da dama a wani wurin taron bikin aure a karamar hukumar Kagarko
- Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta yi tsokaci kan lamarin wanda ya faru a ranar Lahadi, 29 ga watan Maris 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - ’Yan bindiga sun farmaki wani taron bikin aure a ƙauyen Kahir da ke karamar hukumar Kagarko a Jihar Kaduna.
Tsagerun 'yan bindigan sun kashe mutane 13 tare da yin garkuwa da wasu mutane waɗanda ba a tantance adadinsu ba a yayin harin.

Source: Facebook
Wani mazaunin Kagarko, Shehu Bala, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust ta wayar taraho a ranar Litinin, 30 ga watan Maris 2026.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Kaduna
Shehu Bala ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:47 na daren ranar Lahadi, 29 ga watan Maris 2026.
Ya ce ’yan bindigar, waɗanda suka zo da yawa kuma ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47, sun shiga dakin taron bikin ne tare da buɗe wuta, tashar Channels tv ta dauko rahoton.
Shehu Bala ya ƙara da cewa an garzaya da mutane da dama waɗanda suka samu raunukan harbin bindiga zuwa babban asibitin Kagarko, sannan wasu mutane biyu da suka ji rauni mai tsanani an kai su Kaduna.
“Akwai abokaina biyu da suke cikin dakin taron waɗanda su ma suka samu raunukan harbin bindiga yayin farmakin."
“Amma ba za a iya tantance adadin waɗanda aka yi garkuwa da su ba saboda yadda aka riƙa harbe-harbe ba kakkautawa.”
- Shehu Bala
Mutane sun rasa rayuka a harin 'yan bindiga
Wani shugaban al’umma wanda ya nemi a sakaya sunansa shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.
Ya bayyana sunayen wasu daga cikin waɗanda aka kashe kamar haka: Bako Danjuma, Williams Luka, Peter Williams, Joseph Yakubu, Victor Peter da John Dan Asabe.
Sauran kuma su ne Angulu Markus, Maikano Aribi, Douglas John Ado Yakubu, Zaphaniah Alhaji, Joseph Kaddah da kuma Francis Unguwa Doya.
Hakazalika ya ce ’yan bindigan waɗanda suka yi ta’asar ba tare da fuskantar turjiya ba na tsawon kusan sa’a guda, sun kuma fasa wasu shaguna inda suka kwashe kayan abinci da kuma magunguna daga wani kemis.

Source: Original
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
Yayin da aka tuntuɓe shi, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, DSP Hassan Mansur, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa rundunar za ta fitar da cikakken rahoto kan lamarin daga baya a yau.
“Rundunar ba ta kai ga samun cikakkun bayanai kan lamarin da ya faru a kauyen Kahir ba, amma za a samar da cikakken rahoto bayan an kammala tattara bayanai."
- Mansur Hassan
'Yan bindga sun kai hari a asibiti
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci a wani asibiti da ke birnin Akure na jihar Ondo.

Kara karanta wannan
Ana tsaka da zargin Isra'ila da cin zarafin Kiristoci, an ci mutuncin babban Fasto
Yan bindigan sun yi garkuwa da ma’aikatan lafiya a asibitin da ke yankin Oke Ijebu a Akure, babban birnin jihar Ondo yayin harin da suka kai.
Maharan dauke da makamai waɗanda suka kawo harin da misalin ƙarfe 2:00 na dare, sun yi awon gaba da dukkan ma’aikatan da ke bakin aiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

