Jerin Manyan Najeriya da Suka Halarci Jana'izar Mamar El Rufa'i

Jerin Manyan Najeriya da Suka Halarci Jana'izar Mamar El Rufa'i

  • A ranar Lahadi, 29 ga watan Maris, 2026 aka yi jana'izar mahaifiyar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i a birnin tarayya, Abuja
  • Manyan 'yan siyasa, malaman addini da sarakunan gargajiya sun halarci jana'izar domin nuna alhini ga El-Rufa'i bisa babban rashin da ya yi
  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, gwamna Uba Sani, Malam Nuhu Ribadu na cikin manyan kasa da suka halarci jana'izar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A ranar Lahadi, manyan mutane daga bangarori daban-daban sun hallara Abuja domin karrama Hajiya Umma El-Rufai, mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Daga gidansa da ke Abuja zuwa masallaci, sannan zuwa makabartar Gudu, ‘yan jam’iyyun adawa da na gwamnati sun halarci jana'izar domin mika ta’aziyya.

Wajen jana'izar mahaifiyar Nasir El-Rufa'i
Manyan kasa a wajen jana'izar mahaifiyar Nasir El-Rufa'i a Abuja. Hoto: Ismaila Uba Misilli.
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa wasu daga cikin 'yan siyasar da suka halarci jana'izar sun raba hanya da Nasir El-Rufa'i a duk da sun kasance tare a baya.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci sun yi wa Tinubu saukar Kur'ani sama da sau 100

Manyan kasa a jana'izar Umma El-Rufa'i

Gwamnan Kaduna Uba Sani da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, sun halarci gidan El-Rufa'i da kuma sallar jana’izar mahaifiyarsa.

Atiku Abubakar ya wallafa a X cewa ya shaida sallar gawar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023 Peter Obi, tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi ma sun halarci wajen jana'izar.

Tsohon gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal, da tsohon gwamnan Adamawa Jibrilla Bindow, tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, ma sun hallara.

Karin mahalarta jana'izar Umma El-Rufa'i

Gwamnonin jam’iyyar APC ma sun halarta, ciki har da Babagana Zulum da Umaru Bago; tsohon shugaban APC na ƙasa Abdullahi Ganduje; da tsohon ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau, da sauransu.

Haka kuma, Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari, Sanata Shehu Sani da attajirin ɗan kasuwa Aliko Dangote sun halarta.

Yadda aka dauko gawar mamar Nasir El-Rufa'i
Nasir El-Rufa'i ya riko gawar mahaifiyarsa a Abuja. Hoto: Dr Idris Mohammed
Source: Facebook

A lokacin birne marigayiyar a makabartar Gudu da ke Abuja, tsohon ministan sadarwa Isa Pantami ya riƙe El-Rufai da Uba Sani a kafaɗunsu tare da yin wasu kalamai masu ratsa zuciya.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da zargin Isra'ila da cin zarafin Kiristoci, an ci mutuncin babban Fasto

Ya ce:

“Mu mai da hankali kan abubuwan da suka haɗa mu domin sun fi waɗanda suka raba mu yawa. Rayuwa da duk abin da ke cikinta za su ƙare, kabari ne makomarmu. Duk ƙoƙarinka ba za ka samu komai ba sai da yardar Allah.”

Rayuwar El-Rufa'i a hannun ICPC

A wani labarin, kun ji cewa an samu labarin yadda tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya yi rayuwa a hannun hukumar ICPC da ta tsare shi.

Wani makusancin tsohon gwamnan ya sanar da cewa Nasir El-Rufa'i shafe lokacin da ya ke tsare wajen karatun Al-Kur'ani mai girma da wasu littattafai.

Hukumar ICPC ta saki tsohon gwamnan ne a lokacin da aka sanar da rasuwar mahaifiyarsa a kasar Masar domin halartar jana'iza da karbar ta'aziyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng