Malaman Musulunci Sun Yi wa Tinubu Saukar Kur'ani Sama da Sau 100
- Malamai, 'yan siyasa da sarakuna sun taru a Abuja domin taya Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara 74 da haihuwa
- Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da addu'o'i domin samun nasarar shugaba Bola Tinubu da cigaban Najeriya a wani taro a Abuja
- Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa malamai da dama sun taru domin yi wa Tinubu addu'a, inda suka yi saukar Kur'ani sama da 100
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugabannin Musulunci sun gudanar da addu’o’i na musamman domin zaman lafiya da ci gaban Najeriya yayin da Bola Ahmed Tinubu ya cika shekaru 74.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III da Etsu Nupe Yahaya Abubakar ya wakilta, tare da wasu manyan sarakuna da malamai, sun jagoranci addu’o’i na musamman ga shugaba Bola Ahmed Tinubu a masallacin kasa a Abuja.

Kara karanta wannan
Tinubu ya yi abun mamaki, ya sadaukar da dukkan albashinsa na shekaru 3 ga sojoji

Source: Facebook
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa shugaba Tinubu ya isa masallacin bayan ƙarfe 3:00 na rana, inda ya halarci addu’o’in sannan ya yi sallar La’asar kafin ya tafi.
An yi wa Bola Tinubu addu'a a Abuja
Taron addu’ar ya samu halartar gwamnoni, ministoci, ‘yan siyasa da masu ibada daga sassa daban-daban na ƙasar, inda aka mayar da hankali kan roƙon Allah ya ba shugaban hikima, lafiya da ƙarfin gwiwa wajen jagorantar al’amuran ƙasa.
Etsu Nupe ya bayyana taron a matsayin ibada mai muhimmanci, yana mai jaddada bukatar ci gaba da yin addu’a domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.
Rahotanni sun nuna cewa ya kuma roƙi gwamnatin tarayya da ta tallafa wajen kula da buƙatun gyara babban masallacin kasa da ke Abuja.
Haka kuma, Sarkin Keffi, Chindo Yamusa, ya yaba da ƙoƙarin shugaban wajen magance matsalolin tattalin arziki da tallafa wa jihohi, yana mai cewa matakan da aka ɗauka sun fara haifar da alfanu, musamman a jihar Nasarawa.
Malamai sun yi wa Tinubu sauka
A Malaman addinin Musulunci daga kungiyoyi daban-daban sun yi addu’o’i domin samun nasara da lafiyar shugaban da kuma cigaban ƙasa.
A yayin taron, malamai sama da 300 sun yi saukar Alƙur’ani mai girma sau 111, tare da yin addu’o’i na musamman domin ci gaban Najeriya.
Bayanain Sanata Barau Jibrin
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya miƙa godiyar shugaban ga shugabannin addini, jami’an gwamnati da duk mahalarta taron bisa addu’o’i da goyon bayansu.
The Nation ta rahoto ya ce Shugaba Tinubu na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da haɗin kai da ci gaban ƙasa, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da addu’a domin nasarar gwamnatinsa.

Source: Facebook
An kammala taron da Sheikh Ibrahim Maqari ya jagoranta da addu’ar samun zaman lafiya mai ɗorewa, wadata da kwanciyar hankali a Najeriya.
Batun wa'adin mulkin Tinubu na 3
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sarkin Iwo, Oba Abdulrashid Akanbi ya taya Bola Tinubu murnar cika shekara 74 da haihuwa.
Sarkin ya bayyana cewa zai iya yiwuwa 'yan Najeriya su roki a gyara kundin tsarin mulki domin ba Tinubu damar yin wa'adi sama da biyu.
Oba Akanbi ya lissafa wasu muhimman ayyuka da ya ce shugaban kasar ya yi a Najeriya da ya ce sun kawo cigaba sosai da za a amfana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

