'Yan Ta'adda Sun Kai Mummunan Hari Filato, An Kashe Musulmai da Kirista

'Yan Ta'adda Sun Kai Mummunan Hari Filato, An Kashe Musulmai da Kirista

  • Wasu 'yan bindiga kan babura sun kai hari yankin Angwan Rukuba dake Jos ta Arewa inda suka kashe mutane da dama a ranar Lahadi
  • Sai dai bayan tafiyar 'yan ta'addan, an rahoto cewa matasan yankin sun rika tare hanya, suna kashe wa tare da kona matafiya
  • Biyo bayan wannan, gwamnatin jihar Filato ta saka dokar hana fita ta sa'o'i 48 a Jos ta Arewa domin dakile yaduwar tashin hankali

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Wasu miagun 'yan bindiga sun farmaki yankin Angwan Rukuba dake ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.

Shaidun gani da ido sun ce 'yan ta'addan sun farmaki Rukuba ne a daren ranar Lahadi, 29 ga Maris, 2026, inda suka kashe mutane masu yawa.

'Yan bindiga sun kashe mutane a harin da suka kai jihar Filato.
Taswirar jihar Filato, inda 'yan ta'adda suka kashe mutane masu yawa a Angwan Rukuba. Hoto: Legit Hausa.
Source: Original

'Yan bindiga sun kai hari Jos

Kara karanta wannan

Ana tsaka da zargin Isra'ila da cin zarafin Kiristoci, an ci mutuncin babban Fasto

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa maharan sun farmaki yankin ne da misalin ƙarfe 7:30 na yamma, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa:

"Maharan sun zo ne a kan babura suka fara harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya janyo tsoro da firgici a tsakanin mazauna Angwan Rukuba."

Biyo bayan wannan hari, wasu fusatattun matasa a yankin sun toshe manyan hanyoyi, inda rahotanni suka nuna cewa an kashe wasu masu Keke Napep da fasinjojinsu a matsayin ramuwar gayya.

Wannan mataki ya janyo tsananin fargaba a cikin birnin Jos, yayin da mutane suka rinka guduwa zuwa gidajensu domin tsira daga harin ramuwar gayyar da ya biyo baya.

An ayyana dokar hana fita ta awa 48

Gwamnatin jihar Filato, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang, ta sanar da saka dokar hana fita ta sa'o'i 48 a Jos ta Arewa wadda za ta fara aiki daga tsakar daren 29 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu, 2026.

Jaridar The Cable ta rahoto kwamishinar yaɗa labarai ta jihar, Joyce Lohya Ramnap, ta bayyana harin a matsayin abin takaici.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa cikin asibiti, an sace ma'aikatan lafiya

"Gwamnati tana Allah-wadai da wannan hari na rashin tausayi da aka kai wa mutanen da ba su ji ba su gani ba.
"Gwamna Mutfwang ya ba da tabbacin cewa ana ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin kamo waɗanda suka aikata wannan danyen aiki."

- Joyce Lohya Ramnap.

Gwamnatin Filato ta ayyana dokar ta baci ta awa 48 a Jos bayan harin 'yan bindiga
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang zaune cikin damuwa. Hoto: @CalebMutfwang
Source: Facebook

Sojoji sun kai daukin gaggawa a Rukuba

Ma'aikatar yaɗa labarai ta jihar ta yi kira ga mazauna birnin Jos da su kwantar da hankulansu su kuma ba wa jami'an tsaro haɗin kai domin gudanar da bincike yadda ya kamata.

Wannan na zuwa ne yayin da aka rahoto cewa rundunar soji ta "Operation Enduring Peace" ta kai daukin gaggawa Rukuba bayan samun kira daga yankin.

Kakakin rundunar, Kyaftin Polycap Oteh, ya bayyana cewa:

"An tura dakarunmu cikin gaggawa domin maido da doka da oda da kuma hana wannan tashin hankali ya bazu zuwa wasu sassan."

An kashe Musulmi 4700 a Filato

A wani labari, mun ruwaito cewa, Musulmi a Jos sun gudanar da addu’a karo na 17 domin tuna dubban rayukan da aka rasa a tashe-tashen hankula cikin shekaru 20.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda Sanata Shehu Sani ya kwarewa jam'iyyar APC baya

Al’ummar sun ce tun bayan rikicin kananan hukumomi na 2008 da sauran hare-hare da suka biyo baya, rayuka fiye da 4,700 ne suka salwanta.

Shugaban ƙungiyar Jasawa Community Development Association (JCDA), Yawale Muhammad, ya bayyana cewa rikicin Filato ya jawo kisan al’ummar Musulmi masu yawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com