NiMet: Gombe, Bauchi da Jihohin da za Sha Ruwan Sama a Arewa a Yau Litinin

NiMet: Gombe, Bauchi da Jihohin da za Sha Ruwan Sama a Arewa a Yau Litinin

  • Hukumar hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta fitar da hasashen yadda yanayi zai kasance a yau Litinin, 30 ga watan Maris, 2026 a jihohi
  • NiMet ta sanar da cewa za a wayi gari da rana a wasu jihohin Arewacin Najeriya, yayin da za a samu ruwan sama da yamma a wasu
  • Domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a, hukumar ta sanar da matakan da ya kamata kowane mutum ya dauka a yankunan Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Rahoton hasashen yanayi da hukumar NiMet ta fitar na yau Litinin, 30 ga watan Maris 2026 ya nuna cewa za a samu ruwan sama a wasu jihohi.

Hakan na zuwa ne yayin da damuna ta fara dawowa a wasu jihohin Arewacin Najeriya, inda aka samu ruwan sama a wasu yankuna.

Kara karanta wannan

APC tana cikin matsala, maganar tikitin Kwankwaso da Obi ya fara jan hankali

Yadda aka samu ruwan sama a Nafada a Gombe
Yara na wasa yayin da ake ruwa a Nafada, jihar Gombe. Hoto: Jamsy El-nfaty
Source: Facebook

A sakon da NiMet ta wallafa a shafinta na X, Legit Hausa ta gano cewa jihar Gombe na cikin jihohin da ake hasashen samun ruwan sama a yau.

Jihohin Arewa da za a yi ruwa

Hasashen NiMet ya nuna cewa ana sa ran yanayi mai dauke da hasken rana tare da ɗan gajimare a yankunan Arewacin Najeriya da safe.

Daga rana ta daga zuwa yamma, ana sa ran tsawa tare da ruwan sama matsakaici a jihohin Taraba, Kudancin Kebbi, Kudancin Adamawa, Kudancin Zamfara, Kudancin Katsina, Gombe da Bauchi.

Hasashe a wasu jihohin Arewa

A wasu jihohin Arewa ta Tsakiya, rahoton ya nuna cewa za a tashi da zafi da safe sannan a samu tsawa daga baya, inda ake sa ran samun gajimare a yankin.

Hukumar NiMet ta ce ana iya samun tsawa a wasu wurare tare da ruwan sama matsakaici a jihohin Kwara, Niger da Kogi a yau.

Kara karanta wannan

Komai ya fito: Yadda Boko Haram ta saki bama bamai kan masu azumi a Borno

Za a yi ruwa a jihohin Kudu

Hasashen yanayi ya nuna cewa za a samu gajimare tare da hasken rana kadan lokaci bayan lokaci da safe a Kudancin Najeriya.

Daga baya kuma, rahoton ya ce ana iya samun tsawa tare da ruwan sama matsakaici a jihohin Delta, Edo, Cross River, Akwa Ibom

NiMet ta bayyana cewa hasashen ya nuna cewa ana sa ran tsawa tare da ruwan sama matsakaici a duk faɗin yankin da yamma.

Gargadin NiMet ga jama'a

Saboda iska mai ƙarfi na iya fara zuwa kafin tsawa a jihohi, NiMet ta bukaci al'umma su gyara abubuwan da iska za ta iya ɗauka.

Mai Napep yana tafiya a ruwan sama
Yadda mutane ke tafiya a ruwan sama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yayin da aka samu ruwan sama, hukumar ta bukaci a rika tuki a hankali saboda kaucewa zamewa a hanyoyi a lokacin da ake tafiya da babur da sauransu.

Hukumar ta bukaci a cire na’urorin lantarki domin kauce wa lalacewa sakamakon walƙiya, sannan a sha ruwa sosai, musamman a yankunan da ake hasashen samun rana.

Kara karanta wannan

An dasa bam a sansanin sojojin Amurka da ke yaki da Iran

NiMet ta ce za a yi ruwan sama

A wani labarin, mun kawo muku hasashen da hukumar NiMet ta yi game da yadda yanayi ya kasance a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris, 2026.

A jihohin Arewa, hukumar ta sanar da cewa akwai alamun samun ruwa da yamma a jihohin Sokoto, Kebbi bayan an yi rana da safe.

A Kudancin Najeriya kuma, NiMet ta sanar da cewa za a samu ruwa mai yawa a jihohin da suka hada da Legas, Rivers da Bayelsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng