'Yan Bindiga Sun Kutsa cikin Asibiti, an Sace Ma'aikatan Lafiya
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Ondo da ke yankin Kudu maso Yamma na Najeriya
- Tsagerun 'yan bindigan sun kai harin ne a wani asibiti da ke cikin birnin Akure inda suka yi awon gaba da ma'aikatan lafiya
- Jami'an tsaro na Amotekun sun kai daukin gaggawa inda suka samu nasara kan 'yan bindigan da suka kai wannan mugun hari
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Akure, jihar Ondo - ’Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wani asibiti a jihar Ondo.
'Yan bindigan sun yi garkuwa da ma’aikatan lafiya a wani asibiti da ke yankin Oke Ijebu a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce maharan waɗanda suka kawo harin da misalin ƙarfe 2:00 na dare, sun yi awon gaba da dukkan ma’aikatan da ke bakin aiki.

Kara karanta wannan
Sojoji na fifita 'yan bindiga fiye da mutanen da aka zalunta? Rundunar ta magantu
'Yan bindiga sun sace ma'aikatan lafiya
Wani mara lafiya a asibitin ya ce maharan sun zo ne da wata babbar motar bas, inda suka shiga asibitin da ke kusa da makarantar Mega School, suka kwashe ma’aikatan lafiya shida, har da wasu ɗalibai masu neman ƙwarewa.
An ce ’yan bindigan sun tura waɗanda abin ya shafa cikin motar bas ɗin kafin su tsere zuwa inda ba a sani ba.
Jami'an tsaro sun kai dauki
Sai dai kuma, jami’an hukumar tsaro ta jihar Ondo, wadda aka fi sani da Amotekun, sun ceto mutane biyar a wasu samame biyu daban-daban da suka kai a daren jiya a ƙaramar hukumar Akure ta Kudu da ke jihar.
Kwamandan rundunar, Akogun Adetunji Adeleye, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an sace wani mutum ɗan shekara 45 da ɗansa ɗan shekara 15 a Pelebe, da ke bayan garin hanyar Oda-Akure, tsakanin ƙarfe 7:30 na yamma zuwa 8:00 na dare.
Sai dai, jami’an kai ɗauki na gaggawa na rundunar Amotekun sun ceto su da misalin ƙarfe 1:00 na dare bayan wata fafatawa mai tsanani da masu garkuwar, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
An ceto mutanen da aka sace
Adeleye ya ƙara bayyana cewa ma’aikatan lafiya uku da aka sace a baya su ma sun samu ’yancinsu da misalin ƙarfe 4:30 na asuba, kuma a halin yanzu suna karɓar magani a asibitin rundunar Amotekun.

Source: Original
Kwamandan na Amotekun ya tabbatar wa mazauna yankin cewa kare rayuka da dukiyoyi ya kasance babban fifiko ga gwamnatin jihar.
Ya buƙaci jama’a da su ci gaba da samar da bayanan sirri akan lokaci ga hukumomin tsaro, yana mai jaddada buƙatar haɗin gwiwa domin ƙarfafa tsaro a faɗin jihar.
"Ma'aikatan lafiya uku ne kawai aka sace ba shida ba, kuma mutanenmu sun ceto su."
- Akogun Adetunji Adeleye
'Yan bindiga sun kai hari a coci
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wata coci da ke jihar Kwara.
'Yan bindigan sun farmaki cocin ECWA da ke yankin Omugo, a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara, inda suka yi awon gaba da wasu masu ibada.
Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun afka cikin harabar cocin ne tare da sace mutane da dama kafin jami’an tsaro su kawo dauki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
