'Dalilin ICPC na Sakin Nasir El Rufai bayan Rasuwar Mahaifiyarsa'

'Dalilin ICPC na Sakin Nasir El Rufai bayan Rasuwar Mahaifiyarsa'

  • Hukumar yaki da cin hanci da sauran laifuffuka masu alaka (ICPC) ta saki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai
  • Majiyoyi daga hukumar sun bayyana dalilin da ya sanya aka saki El-Rufai bayan ya kwashe kwanaki a tsare
  • Sakin El-Rufai dai na zuwa ne bayan mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai, ta yi bankwana da duniya a birnin Cairo na kasar Egypt

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da sauran laifuffuka masu alaƙa (ICPC) ta saki Nasir El-Rufai.

Hukumar ICPC ta saki tsohon gwamnan na jihar Kaduna ne a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris 2026.

ICPC ta saki Nasir Ahmad El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

Meyasa ICPC ta saki Nasir El-Rufai?

Majiyoyi sun sanar da jaridar The Cable a ranar Asabar, 28 ga watan Maris 2026 cewa hukumar ICPC ta saki El-Rufai saboda dalilai na jin kai da tausayawa sakamakon rasuwar mahaifiyarsa.

Kara karanta wannan

Bayan mutuwar mahaifiyarsa, an saki tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El Rufai

Hajiya Umma, mahaifiyar El-Rufai, ta rasu a ƙasar Egypt inda take jinyar rashin lafiya a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris 2026.

Majiyoyi a hukumar yaƙi da cin hancin sun bayyana cewa an saki El-Rufai ne domin ya samu damar halartar dukkan shirye-shiryen jana'izar mahaifiyarsa.

El-Rufai ya dauki lokaci a hannun ICPC

Tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja ya shiga hannun hukumar ICPC ne a ranar 19 ga watan Fabrairu, bayan da hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) ta sake shi.

A ranar 18 ga watan Maris, ICPC ta ce ta samu halattaccen umarnin kotu na ci gaba da tsare El-Rufai yayin da ake tsaka da kiran da ake yi na a sake shi.

A ranar Talata, 24 ga watan Maris 2026 an gurfanar da El-Rufai tare da Joel Adoga, a babbar kotun tarayya da ke Kaduna kan tuhume-tuhume na zargin halatta kuɗin haram, zamba, da kuma amfani da ofis ta hanyar da ba ta dace ba.

Tsohon gwamnan na Kaduna da Adoga sun musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi musu. Daga baya kotun ta ɗage sauraron buƙatar belinsa zuwa ranar 31 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

El Rufai na iya samun beli don halartar jana'izar mahaifiyarsa? Lauya ya yi bayani

Mahaifiyar Nasir El-Rufai ta rasa
Malam Nasir El-Rufai tare da mahaifiyarsa Hoto: @elrufai
Source: Twitter

An kalubalanci ICPC kan sakin El-Rufai

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, Inibehe Effiong, wani lauya mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, ya ce ICPC ba za ta iya sakin El-Rufai ba tare da amincewar kotu ba.

"Mutumin da aka tura gidan yari ta hanyar umarnin kotu ba za a iya sakin sa ba ta fuskar doka ba tare da komawa ga kotun ba."
"ICPC, ko za ku iya fayyace tsarin da aka bi a wannan shari'ar? An shirya sauraron buƙatar belin El-Rufai ne a ranar Talata, 31 ga watan Maris, 2026."
"Yaya aka bi aka aiwatar da sakinsa? Ko wannan wani siddibarun gwamnati ne wanda shahararren mawaki Fela ya rera waka a kai?"

- Inibehe Effiong

'Dan El-Rufai ya yi raddi ga Uba Sani

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

Dan El Rufai ya kausasa harshe ga Gwamna Uba Sani bayan ya yi ta'aziyyar kakarsa

Da a wajen El-Rufai, Bashir El-Rufai, ya yi watsi da ta'aziyyar da gwamnan na jihar Kaduna ya yi kan rasuwar.

Bashir El-Rufai ya nuna cewa ba sa bukatar ta'aziyyar da Gwamna Uba Sani ya yi kan rasuwar Hajiya Umma El-Rufai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng