Bayan Mutuwar Mahaifiyarsa, An Saki Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El Rufai
- Rahotanni sun bayyana cewa hukumar ICPC ta saki tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma
- An ce tsohon gwamnan ya riga ya bar ofishin hukumar ICPC da ke Abuja, inda yake a tsare tun ranar 19 ga watan Fabrairu, 2026
- Masana shari'a sun bayyana cewa babu inda doka ta ce kotu ta bada belin wanda yake tsare domin ya halarci jana'izar mahaifiyarsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wani labari da ke jan hankali a yanzu shi ne sanarwar da Bashir El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya wallafa na cewa an saki mahaifinsa, Malam Nasir El-Rufai.
Wannan sanarwa tana zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan rasuwar mahaifiyar El-Rufai, Hajiya Umma, wadda ta riga mu gidan gaskiya a yau Jumma'a.

Kara karanta wannan
El Rufai na iya samun beli don halartar jana'izar mahaifiyarsa? Lauya ya yi bayani

Source: Twitter
"An saki mahaifina" - Bashir El-Rufai
Bashir ya bayyana hakan ne ta shafinsa na X (wanda aka sani da Twitter a dā), inda ya nuna farin cikinsa tare da sukar hukumar ICPC.
Ya rubuta cewa:
“Alhamdulillah. An saki ƙasaitaccen mahaifina (@elrufai) daga inda ake tsare da shi ba bisa ƙa'ida ba, a hannun ɗaya daga cikin hukumomin da suka fi cin hanci a Najeriya... Mun yi nasara, kamar yadda iyalin El-Rufai ke yi a ko yaushe.”
El-Rufai ya bar ofishin ICPC
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya riga ya bar ofishin hukumar ICPC, inda yake a tsare tun 19 ga watan Fabrairu, 2026.
Wani makusancin El-Rufai ne ya shaida wa jaridar cewa an saki tsohon gwamnan, amma bai bada wani karin bayani ba.
Wannan ya yi daidai da sanarwar da Bashir El-Rufai ya fitar, wadda ta tabbatar da cewa tsohon ministan Abujan ya shaki iskar 'yanci.
Muhawara kan bada belin El-Rufai
Tun kafin wannan sanarwa ta fito, muhawara ta barke a shafukan sada zumunta game da ko doka za ta ba El-Rufai damar halartar jana'izar mahaifiyarsa.
Don fayyace gaskiyar lamarin, Legit Hausa ta tuntuɓi ƙwararren lauya, Barista Bashir Muhammad Bello, daga rukunin lauyoyi na M.T Mohammed & Co. (Pinnicle Chambers) dake Kaduna.
Barista Bashir ya bayyana cewa, a tsarin doka, rasuwar makusanci ba dalili ne na bayar da beli ba. Ya bayyana cewa:
“Rashi na iyaye, ko 'yan uwa, ko ɗa, ko wani abu da ke kusanci da wanda yake fuskantar shari'a, ba ya daga cikin dalilin ba da beli ko da kuwa na minti biyar ne.”
Ya ƙara da cewa dalilan ba da beli suna ƙunshe ne a cikin dokokin ACJL da ACJA, kuma mutuwa ba ta cikinsu.

Source: Twitter
Shin sakin El-Rufai ya saba wa doka?
Lauyan ya yi nuni da cewa alkali ne kaɗai ke da ikon amfani da huruminsa wajen bayar da beli idan ya ga dacewar hakan saboda yanayin rashi, amma doka ba ta tilasta hakan ba.
Ya jaddada cewa:
“Da ma a ce wanda ake ƙarar ne yake rashin lafiya, to ko don gudun kada ya mutu, ana iya ba da shi beli domin ya ga likita, amma don wani nasa ne ya mutu, to ba za a sake shi don ya je jana'iza ba.”
Malam Nasir El-Rufai yana fuskantar tuhume-tuhume ne kan zargin karkatar da kuɗaɗen sallama na ma'aikata da kuma wasu daloli da aka samu a asusunsa.
'Kuskuren da E-Rufai ya tafka' - Dalung
A wani labari, mun ruwaito cewa, Solomon Dalung ya bayyana cewa Nasir El-Rufai ya nuna dattako wajen mika kansa ga EFCC duk da cewa hakan ya zama babban kuskure.
Ana tuhumar tsohon gwamnan Kaduna kan karkatar da kudaden sallama da suka kai Naira miliyan 579 da kuma boye wasu kudade.
Tsohon ministan matasa da wasanni, Dalung ya yi ikirarin cewa shari'ar El-Rufai ba za ta je ko ina ba domin hukumomin Najeriya ba su da kwararan hujjoji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

