Ta Faru Ta Kare: Mataimakin Gwamnan Kano, Gwarzo, Ya Yi Murabus daga Mukaminsa

Ta Faru Ta Kare: Mataimakin Gwamnan Kano, Gwarzo, Ya Yi Murabus daga Mukaminsa

  • Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam ya yi murabus daga mukaminsa a yau Juma'a, 27 ga watan Maris, 2026
  • Kwankwasiyya ta bayyana cewa Aminu Gwarzo ya yi murabus ne bisa kishin kasa, da son wanzar da zaman lafiya a Kano
  • Gwarzo ya yi martani ga yunkurin da majalisar dokokin jihar ta fara na tsige shi, yana mai cewa bai aikata laifin komai ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Cikin wani babban sauyi na siyasa a jihar Kano, Mataimakin Gwamna Kwamared Aminu Abdussalam ya yi murabus daga muƙaminsa a yau Juma'a, 27 ga Maris, 2026.

Kakakin tafiyar Kwankwasiyya, Dr. Habibu Sale Mohammed, ne ya sanar da hakan ta hanyar wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.

Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Gwarzo ya yi murabus daga mukaminsa.
Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya yi murabus daga mataimakin gwamnan Kano. Hoto: Aminu AbdulSalam Gwarzo
Source: Facebook

Mataimakin Gwamnan Kano ya yi murabus

Kara karanta wannan

Gargadi mai tsauri da Trump ya yi ga kasar Iran kan sharudansa na zaman lafiya

Wannan murabus yana zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta ƙaddamar da tsarin tsige shi daga kan mulki, in ji rahoton Daily Trust.

Ko da yake Kwamared Aminu Gwarzo ya shigar da ƙara a babbar kotun tarayya dake Kano domin dakatar da shirin majalisar, kotun ta yi watsi da buƙatarsa, matakin da ya ƙara matsa masa lamba har ya kai ga sauka daga kan kujerarsa.

Sanarwar ta bayyana cewa Gwarzo ya ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da kuma ba gwamnati damar gudanar da ayyukanta ba tare da tangarɗa ba.

Me ya jawo Aminu Gwarzo ya yi murabus?

Sanarwar Dr. Habibu Sale ta ce:

“Yanayin da ake ciki a yanzu ya kawo cikas ga gudanar da ayyukan ofishin Mataimakin Gwamna yadda ya kamata, shi ya sa ya zama dole a bar ofishin domin ya ci gaba da amfanar al'umma.”

Dr. Habibu ya jaddada cewa wannan murabus ba yana nufin Kwamared Aminu ya amince da zarge-zargen da majalisar dokoki ke masa ba ne.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

Kara karanta wannan

Allah mai iko: Wata mata ta haifi 'yan 5 rigis a Kano, gwamnati ta dauki mataki

“Mataimakin gwamnan ya jaddada cewa ba shi da laifi, kuma tarihin aikinsa shaida ne kan gaskiya da riƙon amana da yake da su ga mutanen jihar Kano.”
An ce mataimakin gwamnan zai mayar da hankali kan ci gaban Kwankwasiyya bayan ya yi murabus.
Gwamna Abba Yusuf tare da Kwamared Aminu Abdulssalam Gwarzo. Hoto: @Kyusufabba
Source: Twitter

Shirye-shiryen babban zaɓen 2027

Bayan barin ofishinsa, sanarwar ta nuna cewa Abdussalam zai mayar da hankali sosai wajen ƙarfafa tafiyar Kwankwasiyya domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen sheƙa da rarraba kawuna a tsakanin manyan jiga-jigan siyasar jihar.

A ƙarshe, jagororin tafiyar sun yi kira ga magoya bayansu da su kwantar da hankulansu su zauna lafiya, tare da bin doka da oda.

Wannan murabus dai ya bar tambayoyi da dama a zukatan Kanawa game da wanda Abba zai naɗa a matsayin sabon mataimakinsa domin kammala ragowar wa'adin mulkinsu.

Kotu ta yi watsi da bukatar Aminu Gwarzo

Tun da fari, mun ruwaito cewa, kotu ta yi watsi da bukatar da mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya shigar gabanta kan yunkurin tsige shi da ake yi.

Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ya kuma buƙaci a dakatar da shirin tsige shi har sai an saurari ƙarar farko da aka shigar a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano.

Sai dai a hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a S.M. Shaibu ya bayyana cewa mai ƙara bai cika sharuddan da ake buƙata domin samun irin wannan umarni na wucin gadi ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com