Sojoji na Fifita ’Yan Bindiga Fiye da Mutanen da Aka Zalunta? Rundunar Ta Magantu
- Hedkwatar tsaro a Najeriya ta yi karin haske kan zargin fifita yan ta'adda ko rangwanta masu kan mutane da ake zalunta
- Rundunar soji ta ce 'Operation Safe Corridor' ba tsarin afuwa ba ce, shiri ne na gyara da dawo da tsofaffin mayaƙa cikin al'umma
- Sojoji sun bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da bayanan karya, su goyi bayan kokarin tsaron kasa da yaki da ta'addanci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hedikwatar tsaron Najeriya ta yi martani mai zafi kan jita-jitar da ake yadawa na nuna rangwame ga yan ta'addada da ke kai hare-hare.
Rundunar ta yi watsi da rade-radin da ke yawo cewa rundunar soji na fifita sassauci ga ‘yan ta’adda maimakon samar da adalci ga wadanda suka jikkata.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na rundunar, Manjo Janar Samaila Uba ya fitar wanda shafin rundunar ya wallafa a X.

Kara karanta wannan
Iran ta yi babban kamu, an gano mutane da ke yada sirrinta ga makiya a yaki da Isra'ila
Sojoji sun magantu kan jita-jita kan ta'addanci
Sojojin sun bayyana cewa irin wadannan rahotanni na kafafen sada zumunta karya ne da aka karkatar da su daga ainihin maganganun shugaban sojoji.
Sanarwar ta ce wasu sakonni sun dauki bangare daya na jawabin shugaban sojin, tare da yin watsi da cikakken ma’anarsa, wanda hakan ya haifar da rudani cewa ana tausaya wa ‘yan ta’adda.
Sojojin sun kara da cewa shirin 'Operation Safe Corridor' ba shirin yafiya ba ne, illa wani tsari ne na sauya tunani, gyara da sake mayar da tsofaffin mayaƙa cikin al’umma.
An bayyana cewa wannan shiri yana daga cikin dabarun yaki da ta’addanci da ke hada matakan soja da kuma hanyoyin zaman lafiya, wanda ya taimaka wajen rage karfin kungiyoyin ‘yan tada kayar baya.
Hedikwatar tsaron ta kuma jaddada cewa rundunar sojin Najeriya na ci gaba da daukar matakin murkushe ‘yan ta’adda tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin kasar.
A karshe, ta bukaci ‘yan Najeriya su rika dogaro da sahihan bayanai daga majiyoyi na hukuma, tare da goyon bayan kokarin da sojoji ke yi na tabbatar da tsaro a kasa.

Source: Facebook
Yadda aka juya maganar hafsan tsaro
Sanarwar ta kara bayyana cewa an juya kalaman Babban Hafsan Tsaro ne a yayin wani jawabin ƙa’idojin aikin soja na ƙwararru, inda ya jaddada muhimmancin warware rikice-rikice ta hanyoyi masu fuskoki da dama.
“Wannan bayani ba kawai kuskure ba ne, har ma yana raunana kokarin da ake yi na tabbatar da tsaron kasa a halin yanzu.
"Maganganun hafsan tsaro sun nuna cewa kokarin gyaran hali yana taimaka wa nasarorin da ake samu a fagen daga, ba wai yana maye gurbinsu ba."
Ta'addanci: Najeriya ta kulla alaka da China
An ji cewa majiyoyi sun nuna rundunar sojin saman Najeriya da dakarun kasar China sun jaddada aniyar cigaba da alaka tare domin karfafa juna.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu sojojin kasar China suka ziyarci Shugaban rundunar sojin saman Najeriya, Sunday Kelvin Aneke.
A shekarar 2025 ma dai rundunar sojin saman Najeriya ta ziyarci kasar China, inda suka tattauna manyan abubuwan da suka shafi inganta tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
