Saraki Ya Wanke Tinubu kan Hannu a Abin da Ya Faru da Shi a Gwamnatin Buhari

Saraki Ya Wanke Tinubu kan Hannu a Abin da Ya Faru da Shi a Gwamnatin Buhari

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya tuna baya kan abubuwan da suka faru da shi a gwamnatin Muhammadu Buhari
  • Bukola Saraki ya wanke shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu daga zargin ya taka rawa wajen ganin an tuhume shi
  • Tsohon shugaban majalisar dattawan ya nuna cewa Tinubu bai da irin wannan tasirin a wancan lokacin

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya wanke Shugaba Bola Tinubu kan tuhumar da aka yi masa a mulkin Muhammadu Buhari.

Bukola Saraki ya ce Shugaba Bola Tinubu ba shi da hannu a shari’ar da aka yi masa lokacin gwamnatin marigayi tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

Bukola Saraki ya wanke Tinubu daga zargi
Bukola Saraki da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Abubakar Bukola Saraki, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a shirin 'Politics Today' na tashae Channels Tv a yammacin ranar Alhamis, 26 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Rigima sabuwa: Matakin da shugaban PDP ya dauka bayan kotu ta umarci a cafke shi

BukolaSaraki ya wanke Shugaba Tinubu

Saraki ya yi watsi da iƙirarin da ake yi na cewa Tinubu yana da wani tasiri mai ƙarfi a lokacin gwamnatin Buhari.

A watan Satumban 2015, hukumar kula da da'ar ma’aikata (CCB) ta shigar da ƙara kan zargin rashin bayyana kadarori na ƙarya a kan Saraki a gaban kotun ɗa’ar ma’aikata (CCT).

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce ba adalci ba ne a zargi Tinubu da kasancewa ɓangare na ƙalubalen da ya fuskanta a wancan lokacin.

Saraki ya ce Tinubu bai da tasiri

Bukola Saraki ya yi nuni da cewa an hukunta shi ne saboda ɗaukar matakan da suke “domin amfanin Najeriya”.

“Wannan kuma ba adalci ba ne ga Shugaba Ahmed Bola Tinubu domin ni da kai mun sani cewa a wancan lokacin na gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, ba shi da wancan ikon da suke iƙirarin yana da shi."
“Damuwata ita ce ina yin abin da nake ji yana da amfani ga ƙasa a matsayina na shugaban majalisar dattawa, kuma saboda yin waɗancan abubuwan, sai aka gurfanar da ni.”

Kara karanta wannan

Turaki ya faɗa matsala: Kotu ta bada umarni a kamo shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa

“Bola Tinubu ba ya ɗaya daga cikin mutanen da suka yanke shawara kuma suka aiwatar da batun tafiya kotun ɗa’ar ma’aikata ko fashin Offa ko kuma batun jabun takardu na majalisar dokoki ta ƙasa. Wannan ɓangaren zartarwa ne na gwamnati.”

- Bukola Saraki

Saraki ya wanke Tinubu
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki Hoto: Abubakar Bukola Saraki
Source: Facebook

Me Saraki ya ce kan gwamnatin Tinubu?

Game da ayyukan gwamnatin Tinubu, Saraki ya ƙi bayar da amsa guda, inda ya nuna cewa sakamakon ya kasance mabanbanta a sassa daban-daban.

“Wannan tambaya ce mai wahala saboda akwai abubuwa da dama kuma akwai batutuwa da dama. Akwai abubuwan da zan ce ba sa yin kokari ba a kai. Akwai abubuwan da ba sa yin abin kirki ko kaɗan a kai."

- Bukola Saraki

Saraki ya ba PDP shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya ba jam'iyyar PDP shawara kan rikicin da ya addabe ta.

Bukola Saraki ya bada shawarar a kafa kwamitin rikon kwarya domin ya karɓi ragamar jagorancin PDP.

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya gargadi jam’iyyar cewa ci gaba da shirya taron na Ibadan kamar yadda aka tsara zai kara ta’azzara rikicin da ake cik

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng