Ana Shirin Zaben 2027, Shugaban INEC Ya Hango Abin da Ke Barazana ga Najeriya

Ana Shirin Zaben 2027, Shugaban INEC Ya Hango Abin da Ke Barazana ga Najeriya

  • Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya yi tsokaci kan yanayin gudanar da zabe a Najeriya
  • Farfesa Joash Amupitan ya koka kan yadda ake kara samun yawaitar rashin fitowar masu kada kuri'a a lokacin zabe
  • Shugaban na INEC ya bayyana cewa hakan babbar barazana ce ga tsaron Najeriya domin zai bude kofar da za a iya aikata barna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya yi magana kan zabubbuka a Najeriya.

Joash Amupitan ya yi gargaɗin cewa raguwar yawan masu fitowa zaɓe a Najeriya yana sauyawa daga batun haƙƙin ɗan ƙasa zuwa wani babban al'amari na tsaron ƙasa.

Shugaban INEC ya koka kan zabe a Najeriya
Shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Joash Amupitan Hoto: @inecnigeria
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Amupitan ya yi waɗannan kalaman ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris 2026 a Abuja yayin da yake jawabi a taron bita na shekara-shekara na biyu na ƙungiyar tsofaffin ɗaliban kwalejin tsaro ta ƙasa (AANISS).

Kara karanta wannan

Turaki ya faɗa matsala: Kotu ta bada umarni a kamo shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa

Wadanne maganganu shugaban INEC ya yi?

Shugaban na INEC ya bayyana illolin da ƙarancin sha'awar fitowa zaɓe ke da shi ga shugabanci da daidaiton ƙasa.

“Duk da yadda aka gudanar da zaɓubbukan ƙananan hukumomin birnin tarayya Abuja cikin lumana, inda yawan masu zaɓe ya ƙaru daga kashi 9.4 zuwa kashi 15, rashin sha'awar fitowa zaɓe ya kasance babban ƙalubale mai ban tsoro."

- Farfesa Joash Amupitan

Wace barazana hukumar INEC ta hango

Shugaban na INEC ya nuna cewa ci gaba da raguwar masu fitowa zaɓe tsawon shekaru yana nuna wani yanayi mai matsala babba wanda zai iya raunana halaccin tsarin dimokuraɗiyya, jaridar Leadership ta kawo labarin.

“Raguwa daga kashi 53 a shekarar 2011 zuwa kashi 26 a shekarar 2023, ƙarancin fitowa zaɓe ya fi ƙarfin damuwa ta haƙƙin ɗan ƙasa kawai, barazana ce ga tsaro."
"Rashin sha'awar fitowa zaɓe yana samar da gurbin da baragurbi ke amfani da shi wajen kawo matsala ga gwamnati."

Kara karanta wannan

Ana tsakiyar barin wuta, Najeriya za ta amfana da yakin Amurka, Isra'ila da Iran

- Farfesa Joash Amupitan

Amupitan ya jaddada cewa sahihin zaɓe yana da alaƙa ta kusa da tsaron ƙasa, inda ya bayyana cewa amincewa da tsarin zaɓe yana taka rawar gani wajen hana tarzoma da rashin natsuwa bayan zaɓe.

“Idan ’yan ƙasa suka amince da tsarin zaɓe, sun fi karkata ga amincewa da sakamakon, wanda hakan ke rage takaddamar da za ta iya kai wa ga tarzoma."

- Farfesa Joash Amupitan

Amupitan ya yi magana kan zabubbuka a Najeriya
Farfesa Joash Amupitan a wajen taron hukumar INEC Hoto: @inecnigeria
Source: Facebook

Joash Amupitan ya ba da tabbaci

Haka zalika, ya bayyana wasu sababbin barazana ga sahihancin zaɓe a Najeriya, musamman ƙaruwar tasirin fasaha da yaɗa labaran ƙarya.

To sai dai kuma, Amupitan ya ba wa ’yan Najeriya tabbacin cewa hukumar tana ɗaukar matakai don ƙarfafa sahihanci da gaskiya a zaɓubbukan nan gaba, musamman gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Matsayar INEC kan zaben 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya yi magana kan zaben 2027.

Kara karanta wannan

EIBIC: Gwamnatin Najeriya ta kawo shirin ba matasa horo da ba su jari

Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya ce ba za su iya ba da tabbacin samun zaɓe cikakke 100% a shekarar 2027 ba.

Shugaban na INEC, ya bayyana cwa duk da ƙoƙarin da suke yi, ba za su iya cewa komai zai tafi daidai ba ba tare da tangarda ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng