Damuna Ta Dawo: Sokoto da Wasu Jihohin da ake Tsammanin Ruwan Sama a Yau
- Hukumar hasashen yanayi ta kasa da aka sani da NiMet ta fitar da bahasi kan yadda yanayi zai kasance a yau Juma'a, 27 ga Maris 2026
- Ta lissafa wasu johohin Najeriya kamar Taraba, Kebbi, da sauransu da za a yi rana sosai da safe amma ake tsammanin ruwa da yamma
- NiMet ta bayyana wasu jihohin kudancin Najeriya da suka hada da Rivers, Bayelsa, Legas da sauransu da ake sa ran samun ruwan sama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta sanar da cewa za a iya samun ruwan sama a wasu jihohin Najeriya a yau Juma'a, 27 ga Maris 2026.
NiMet ta bayyana wasu matakai da ya kamata 'yan Najeriya su dauk domin kare kansu daga yanayin da za a iya shiga a jihohi.

Source: Getty Images
Legit Hausa ta tattaro bayanan da hukumar hasashen yanayin ta yi ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook da yammacin Alhamis.
Jihohin da za a yi rana da ruwa
Hasashen hukumar NiMet ya nuna cewa za a yi rana sosai a wasu jihohin Arewa kamar Taraba, Kebbi, Zamfara, Sokoto da Kaduna.
Ana sa ran safiya za ta kasance mai cike hasken rana sosai sannan a iya samun tsawa a wasu wurare a jihohin da aka ambata, wanda za a iya samun ruwa daga baya ko akasin haka.
A wasu jihohin Arewa ta tsakiya kuma, NiMet ta sanar da cewa za a yi zafi da safe sannan tsawa ta biyo baya, inda ta ce za a samu gajimare daga baya.
Hasashen ya nuna cewa ana sa ran tsawa tare da ruwan sama mai sauƙi a jihohin Benue, Niger, Kwara, Plateau, Nasarawa, Kogi da birnin tarayya, Abuja da yamma.
Hasashen NiMet a jihohin Kudu
NiMet ta bayyana cewa za a samu karuwar ruwan sama a wasu jihohin Kudu, inda ta ce za a samu gajimare tare da ɗan hasken rana lokaci-lokaci.
Ta ce ana iya samun tsawa da ruwan sama mai sauƙi a jihohin Ondo, Ogun, Rivers, Bayelsa, Lagos, Akwa Ibom, Cross River a yau da safe.

Source: Original
Zuwa yamma kuwa, hukumar ta ce tsawa za ta ƙaru tare da ruwan sama matsakaici a jihohin Enugu, Anambra, Imo, Abia, Edo, Ebonyi, Oyo, Ogun, Ekiti, Ondo, Osun, Delta, Lagos, Cross River, Akwa Ibom, Bayelsa, Rivers.
Gargadin da NiMet ta yi
Hukumar ta bukaci a guji zama a filin da ya ke a bude kuma kada a tsaya ƙarƙashin manyan itatuwa yayin da ake tsawa domin tsira da rai.
Ta bukaci a cire na’urorin lantarki kafin ruwan sama domin kauce wa lalacewa sakamakon walƙiya sannan kuma a sha ruwa sosai, musamman a Arewa inda zafi zai yi yawa.
Matsalar lantarki ta karu a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa ministan makamashi na kasa, Bayo Adelabu ya sanar da cewa matsaloli da dama ne suka haifar da karancin wuta a kasar nan.
Bayo Adelabu ya ba 'yan Najeriya hakuri tare da bayyana cewa gwamnati ta dukufa domin ganin ta shawo kan matsalar cikin gaggawa.
Ministan ya sanar da cewa yakin da ake a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila na iya kara dagula matsalar lantarki a Najeriya.
Asali: Legit.ng


