'Haram ne': Malami Ya Kalli Sarakuna Ido da Ido, Ya ce Kiransu da Sarki Sabon Allah ne
- Malamin Musulunci a Najeriya ya yi gargadi ga al'ummar Musulmi kan ci gaba da kiran Sarakuna da sunan Sarki
- Sheikh AbdulRazzaq Alaro ya tayar da kura bayan ya ce kiran sarakunan Yarbawa da “Kabiesi” ya saba wa koyarwar Musulunci
- Ra’ayinsa ya haifar da cece-kuce, inda wasu ke ganin magana ce ta addini, yayin da wasu ke kare al’adar Yarbawa a matsayin girmamawa kawai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Fitaccen malamin Musulunci, Farfesa AbdulRazzaq AbdulMajeed Alaro, ya jawo cece-kuce bayan ya ce kiran sarakunan Yarbawa da “Kabiesi” ya sabawa koyarwar addini.
Malamin ya ce kiran basarake da sunan Sarki ya saba wa koyarwar addinin Musulunci kuma haram ne.

Source: Facebook
Malami ya ja kunnen Musulmi a gaban sarakuna
Malamin ya bayyana haka ne a wani wa’azi da ya gabatar lokacin Ramadan, inda ya ce kalmar tana ba dan Adam sifar da ta dace da Allah shi kadai, cewar rahoton Legit.ng.
Shehin malamin ya bukaci sarakunan gargajiya su hana mabiyansu amfani da wannan suna, yana mai cewa Alkur’ani ya haramta bai wa wani halitta irin wannan matsayi.
Sai dai maganar ta fusata wasu masu bin addinin gargajiya, inda wani mai suna Olalekan Awogbemi ya ce kalmar girmamawa ce kawai ba Allahntaka ba.
Awogbemi ya ce malamai kan yi amfani da fassara kai tsaye daga littattafansu wajen sukar al’adun gargajiya ba tare da fahimtar asalin su ba.
Ya kara da cewa a tarihin Daular Oyo, ko Sarkin Alaafin yana da masu duba halayensa, wanda ke nuna cewa yana da saukin kai.
Haka kuma ya bayyana cewa kalmar “Kabiesi” ta samo asali ne daga “Kabi o si”, wadda ke nuna girmamawa.
A karshe, ya bukaci malamai su yi bincike sosai kan al’adun gargajiya kafin su soki su, domin kaucewa yada bayanai marasa inganci.
“Shin ya dace a rika kiran sarakuna da shugabannin gargajiya a ƙasar Yarbawa da suna ‘Kabiesi’? A gaskiya, ina roƙon ku ku fahimce ni, akwai aya a cikin Alƙur’ani game da wannan batu, kuma amsar tana cikinta.
"A cikin ayar, Allah ya ce ba a ba za a kalubalance shi ba. Daga ɗan fahimtata ta harshen Yarbanci, wannan sifar da Allah ke nufi a cikin ayar ita ce ‘Kabiesi’ da muke ba sarakunanmu da shugabannin gargajiya.
"Allah ya bayyana cewa wannan sifa ta keɓanta gare Shi kaɗai.”
'Ya ware kudi': Malami ya zargi Tinubu kan zabe
Kun ji cewa malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Sanusi Khalil ya ce an ware kimanin N500bn domin shirye-shiryen samun nasara a zaben 2027 da ke tafe nan ba da jimawa ba.
Malamin ya ce an shirya kafa kwamiti na malaman addini da sarakunan gargajiya, inda ya ce wani fasto ne zai jagoranta inda ya ce ya yi watsi da tayin daaka yi masa.
Shehin ya bayyana cewa an nemi ya shiga cikin shirin amma ya ce ba shi da hannu a ciki inda ya yi watsi da su tare da jan kunnen malamai da al'umma da su yi hankali.
Asali: Legit.ng

