Isra'ila Ta Yi Rashi yayin da Sojojinta Suka Gwabza da Mayakan Hezbollah, Netanyahu Ya Shiga Jimami

Isra'ila Ta Yi Rashi yayin da Sojojinta Suka Gwabza da Mayakan Hezbollah, Netanyahu Ya Shiga Jimami

  • Mayakan Hezbollah da dakarun sojojin Isra'ila na ci gaba da yin ba ta kashi a wasu yankuna da ke Kudancin Lebanon
  • A wani artabu da aka yi tsakanin bangarorin biyu, mayakan Hezbollah sun samu nasarar hallaka wani sojan Isra'ila har lahira
  • Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi jimamin rashin sojan tare da aika sakon ta'aziyya ga iyalansa

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Beirut, Lebanon - Dakarun sojojin rundunar tsaron Isra'ila (IDF), na ci gaba da fafatawa da mayakan Hezbollah a Kudancin Lebanon.

Wani soja ya mutu a lokacin da ake musayar wuta da mayakan Hezbollah a Kudancin Lebanon a daren ranar Laraba, 25 ga watan Maris 2026.

Hezbollah ta kashe sojan Isra'ila
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da sojan Isra'ila da aka kashe Hoto: @netanyahu
Source: Twitter

Jaridar The Times of Israel ta ce rundunar IDF ta tabbatar da mutuwar sojan a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Makaman da Iran ta harba sun gigita Isra'ila, an ji barnar da suka yi

Kisan sojan na zuwa ne yayin da kungiyar Hezbollah take ci gaba da harba rokoki da jirage marasa matuka kan birane da garuruwan Arewacin Isra'ila.

Hezbollah ta kashe sojan Isra'ila

Sojan da aka kashe an bayyana sunansa da Staff Sgt. Ori Greenberg, dan shekara 21, daga rukunin bincike na dakarun Golani, mazaunin Petah Tikva.

Shi ne soja na uku na IDF da aka kashe a sabon farmakin kasa da Isra'ila ta kaddamar kan Hezbollah a Kudancin Lebanon.

A cewar binciken farko na IDF kan lamarin, da misalin karfe 2:00 na dare, sojojin Golani sun hango wasu mayakan Hezbollah a yankin da suke gudanar da ayyukansu a kudancin Lebanon.

Sojojin Isra'ila na fafatawa da mayakan Hezbollah

Dakarun sun yi musayar wuta da mayakan na Hezbollah, kuma a lokacin fafatawar, aka kashe Greenberg yayin da wani soja guda daya ya ji rauni kadan.

Rahoton ya ce Rundunar IDF ta ce sojan da ya ji raunin bai bukaci kwanciya a asibiti ba.

Mahaifinsa ya bayyana cewa:

"Ori yaro ne da ya shawo kan duk wani cikas da duk wani tsoro da yake da shi. Kullum yana tura kansa gaba da kishin kasa, da soyayya, da kuma kyakkyawar zuciya. Kuma sun gaya mana cewa haka ya hadu da mutuwarsa."

Kara karanta wannan

Iran ta saki bidiyon lokacin da ta harba makami zuwa Isra'ila da barnar da ya yi

Benjamin Netanyahu ya yi ta'aziyya

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi jimamin rasa ran sojan da aka yi Lebanon.

Netanyahu ya yi jimamin sojan Isra'ila da aka kashe
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: @netanyahu
Source: Twitter

A wani rubutu a shafinsa na X ya bayyana cewa:

"Ni da matata, tare da dukkan ƴan ƙasar Isra'ila, muna taya iyalan jarumin dakarun Sayeret Golani, Staff Sergeant (Sgt.) Uri Greenberg, baƙin cikin rashin sa da aka yi, bayan da ya mutu a yaƙin da ake yi a kudancin Lebanon."
"Muna miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayi Uri, wanda ya yi yaƙi cikin jarumta da gaba gaɗi domin kare iyakokinmu na Arewa."

- Benjamin Netanyahu

Isra'ila ta kashe kwamanda a Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ta hallaka babban kwamandan sojojin ruwa na rundunar IRGC ta Iran.

Rundunar IDF ta hallaka Alireza Tansgiri ne yayin wani hari da ta kai a garin Bandar Abbas da ke gabar teku.

Kisan na sa ya kara adadin manyan jagorori da kwamandojin Iran da Isra'ila ta kashe tun bayan fara yaki a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng