Yaki da Ta'addanci: Sojojin Najeriya da China Sun Zurfafa Alakar Tsaro
- Rahoto ya nuna cewa rundunar sojin saman Najeriya da dakarun kasar China sun jaddada aniyar cigaba da alaka tare domin karfafa juna
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu sojojin kasar China suka ziyarci shugaban rundunar sojin saman Najeriya, Sunday Kelvin Aneke
- A shekarar 2025 ma dai rundunar sojin saman Najeriya ta ziyarci kasar China, inda suka tattauna manyan abubuwan da suka shafi inganta tsaro
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Dakarun sojin Najeriya da na kasar China sun yi wata ganawa a Abuja a wani shirin na cigaba da karfafa alakar da ke tsakaninsu.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke cigaba da yaki da 'yan bindiga a Arewa ta Yamma da 'yan Boko Haram a Arewa maso Gabas.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin muhimman abubuwan da sojojin suka tattauna ne a wani sako da rundunar sojin saman Najeriya ta wallafa a X.
Sojojin Najeriya sun hadu da na China
Bayanai sun nuna cewa rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta sake jaddada aniyarta na ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da ƙasar China.
Hakan na zuwa ne bayan wata ziyarar girmamawa da jami’in tsaron ƙasar China, Kanal Ouyang Haisheng ya kai wa shugaban sojin sama, Sunday Kelvin Aneke, a hedikwatar NAF da ke Abuja a ranar 25 ga Maris, 2026.
Muhimmancin taron ga Najeriya
Najeriya ta ce taron ya nuna muhimmancin ci gaba da diflomasiyyar tsaro wajen inganta horo, haɗin gwiwar fasaha da bunƙasa ƙwarewar aiki, musamman wajen tinkarar ƙalubalen tsaro na zamani.
Aneke ya bayyana cewa haɗin gwiwar soja na ƙasa da ƙasa na da muhimmanci wajen sauya fasalin rundunar NAF, domin gina runduna mai ƙwarewa da za ta iya gudanar da ayyukan soji yadda ya kamata.
Rundunar sojin saman ta kara da cewa taron zai kara karfafa hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, tare da taimakawa zaman lafiya a duniya baki ɗaya.

Source: Facebook
Ganawar Najeriya da China a 2025
A watan Agustan 2025 ma dai tsohon shugaban sojin sama, Hasan Abubakar, ya bayyana cewa NAF na ƙara zurfafa haɗin gwiwar tsaro da kasar China.
Vanguard ta rahoto ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara ta aiki ta mako guda da ya kai zuwa kasar China, inda ya jagoranci wata babbar tawagar Najeriya.
A cewar Mai magana da yawun rundunar, tawagar ta gana da manyan kamfanonin jiragen sama da tsaro a biranen Beijing, Haerbin da Chengdu, inda aka tattauna kan fasaha, tallafin gyara jirage da kuma horar da jami’an NAF.
Donald Trump zai kai ziyara China
A wani rahoton, mun kawo muku cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya saka sabuwar ranar da zai kai ziyara kasar China.
Fadar White House ta sanar da cewa Donald Trump zai gana da shugaban kasar China domin tattauna wasu muhimaman abubuwa.
A watan Maris na 2026 Donald Trump ya tsara zai ziyarci kasar China amma ya sauya lokaci zuwa watan Mayu saboda yaki da Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

