Wata Sabuwa: An Yi Amfani da 'Wike' wajen Damfarar Janar Miliyoyi a Abuja
- Rahotanni sun bayyana cewa an kama wasu mutane da ake zargi sun yi amfani da sunan Ministan Abuja, Nyesom Wike sun yi damfara
- Rundunar 'yan sanda ta kama mutane hudu daga cikinsu, inda aka ce sun hada kai sun damfari wani tsohon jami'in sojan Najeriya miliyoyin Naira
- Hukumomi sun bayyana sunayen mutanen da aka kama tare da tabbatar da cewa ana cigaba da bincikensu domin daukar mataki na gaba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa asirin wasu mutane ya tonu bayan shirya damfara da sunan ministan Abuja, Nyesom Wike.
An kama mutanen ne bayan da suka yi dabaru suka raba wani tsohon Janar na sojan Najeriya makudan kudi kan mallakar fili a Abuja.

Source: Facebook
Rahoton the Cable ya nuna cewa 'yan sanda sun yi karin haske game da halin da ake ciki da matakan da ake dauka kan wadanda aka kama.
An yi damfara da sunan Nyesom Wike
Rundunar ‘yan sanda a Abuja ta kama wasu maza huɗu bisa zargin amfani da sunan ministan babban birnin tarayya (Abuja), Nyesom Wike, domin damfarar wani tsohon babban jami’in soja kuɗi har Naira miliyan 150.
A cewar wata majiya, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi, Yashim Kajang, a ranar Talata damfarar da aka ce ta shafi A. K. Ibrahim da wasu mutane a Abuja.
Rahoton ya ce Kajang ya yaudari waɗanda abin ya shafa da cewa yana aiki da Ministan Abuja, inda ya karɓi sama da Naira miliyan 150 daga hannunsu domin samar musu da takardun fili na lamba 1985 da ke Guzape II mai girman hekta uku, da wasu filaye.
Mutanen da 'yan damfaran suka lissafa
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa wadanda ake zargin sun ambaci wasu ma'aikata a Abuja da suka ce tare suke aiki a lokacin da suke tsara damfarar.
“Bayan tambayoyi, wanda ake zargin ya ambaci Stephen Mhambe da Danladi Jatau, dukkansu daga sashen tsara birane na hukumar gudanar da babban birnin tarayya (FCDA), da kuma Terngu Ipaven, mazaunin, Chief Palace Road, Durumi 2, Abuja, a matsayin abokan aikinsa,”
- Inji rahoton

Source: Original
Sauran wadanda ake zargi da damfarar
Rahoton ya ƙara da cewa Kajang ya amsa cewa sauran waɗanda ake zargin, Mhambe, Jatau da Ipaven ne suka ba shi bayanai da takardun filaye da aka yi amfani da su wajen wannan damfarar.
“Mutanen huɗun na ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin bincike,”
Inji rahoton.
An kama dan damfara a Kaduna
A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar 'yan sandan Najeriya a Kaduna ta kama wani matashi da ake zargi da zama dan damfara.
Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin matashin da kwaikwayon muryar gwamnoni domin yaudarar mutane da dama a fadin kasar nan.
Rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa an same shi da lambobin wayar manyan mutane a Najeriya da yake amfani da su wajen yaudarar al'umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

